Yan Kannywood sun yi jimamin cika shekara uku da mutuwar Dan Ibro

Yan Kannywood sun yi jimamin cika shekara uku da mutuwar Dan Ibro

- Fitaccen dan fim din Kannywood Rabilu Musa Dan Ibro ya cika da shekaru uku da mutuwa

- Manyan yan fim sun bayyana irin alakar da ke tsakanin su da shi, da kuma kywawan halayen sa

- Jaruman Kannywood sunyi jimamin cika shekaru uku da mutuwa

Jaruman fina-finan Hausa na Kannywood sunyi jimamin cika shekaru uku da mutuwar fittacen dan wasan barkwanci Rabilu Musa (Dan Ibro).

Dan Ibro ya rasu ne ranar 10 ga watan Disamba na shekara 2014 a bayan ya yi fama da ciwon koda a asibti.

Wasu daga cikin jaruman fina-finan hausa sun bayyana irin dangantakar da ke tsakanin su da Dan Ibro da kuma irin kyawawan halayen sa.

Yan Kannywood sun yi jimamin cika shekara uku da mutuwar Dan Ibro
Yan Kannywood sun yi jimamin cika shekara uku da mutuwar Dan Ibro

Babban furodusan Kannywood Falalu Dorayi ya rubuta a shafin sa na Instgaram cewa “Shekaru uku kenan, 10th December 2014 da rasa abokin neman halak. Innalillahi wa’aina ilaihi Rajiun.

KU KARANTA : Yara dubu 170 ke hawa yanar gizo a kullum - UNICEF ta yi gargadi

"Allah ya jikan ka Rahma alhaji Rabilu Musa Dan Ibro. Allah ya sa haske da ni'ima a cikin kabarinka. Allah yai mana rahma baki daya. Allahu akbar. Rashin da babu madadinsa."

Abdulmumuni Tantiri, wanda suka fito a fim din karshe da Ibro kafin ya mutu, yace “Alhaji Rabilu Musa (Dan Ibro) mutum ne mai kishin sana’ar sa da abokan sa, kuma baya saka bakin sa akan abun da bai shafe sa ba.

Jarumi Ali Nuhu ya rubuta a shafin sa na Instagaram kamar cewa “Sarki Sarki ne har abada. Muna kewarka Chairman.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: