Mun cika alkawuran da muka yiwa yan Najeriya a dukkan bangarori, musamman gidaje: Buhari

Mun cika alkawuran da muka yiwa yan Najeriya a dukkan bangarori, musamman gidaje: Buhari

Benin - Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa ta cika alkawuran da ta yiwa yan Najeriya a shekarar 2015 a dukkan bangarori, musamman gidaje.

Ya bayyana hakan ne ranar Alhamis, yayin kaddamar da gidaje 68 da ma'aikatar gidaje da ayyuka ta gina a titin Benin-Auchi, jihar Edo.

Buhari wanda ya samu wakilcin ministan lafiya, Dr Osagie Ehanire, yace:

"Lokacin da jam'iyyarmu All Progressives Congress (APC), ta bukaci goyon bayanku a 2015, mun yi alkawarin zaku ga canji. Wannan rukunin gidajen misalin ne cika alkawarin da muka yi."
"Ko shakka babu ba zamu iya biyan kowani da Najeriya ba daya bayan daya, amma kudin da muke zubawa cikin manyan ayyuka da tsare-tsare irin na gidajen nan zai isa ga kowa."

Kara karanta wannan

Harin 'yan bindiga a Plateau: Ya zuwa yanzu mun binne mutane 106, inji shugaban karamar hukuma

Ya ce a jihohin da aka yi ire-iren wadannan gine-gine, an mika hakkin kula da gidajen ga wasu kamfanoni domin tabbatar da basu lalace ba, kuma hakan samar da aikin yi ne ga yan Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Buhari
Mun cika alkawuran da muka yiwa yan Najeriya a dukkan bangarori, musamman gidaje: Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel