Bidiyoyin 'yan fim suna shagali a kamun Furodusa Maishadda da Jaruma Hassana Muh'd
1 - tsawon mintuna
- Bidiyoyin shagulgula tare da bidirin bikin kamun Furodusa Abba Maishadda tare da masoyiyarsa Hassana Muhammad sun fara bayyana
- Bikin kamun ya samu halartar jaruman masana'antar har da fitattun mawaka irinsu Ado Gwanja wadanda suka nishadantar da jama'a
- Za a daura auren masoyan ne a ranar 13 ga watan Maris wanda yayi daidai da ranar Lahadi a garin Gombe da ke arewa maso gabas a Najeriya
Shagalin bikin Furodusa Abubakar Maishadda da jaruma Hassana Muhammad ya kankama inda aka yi bikin kamunsu a ranar Juma'a.
Babu shakka biki ya yi biki tunda an ga jarumai mata da maza, mawaka da jiga-jigai daga masana'antar Kannywood sun hallara.

Asali: Instagram
Daga cikin bidiyoyin da Legit.ng ta samo, an ga mawaki Ado Gwanja yana wake ango inda yake ta masa barin dukiya yayin daga bisani mawakin ya koma wakarsa a filin bikin.
Ga wasu daga cikin bidiyoyin a kasa ku sha kallo:
Kamar yadda katin gayyatar bikin ya nuna, za a daura auren masoyan ne a ranar 13 ga watan Maris a garin Gombe.
Asali: Legit.ng
Tags: