Zargin lalata: Kungiyar matan Kannywood ta ba Naziru sarkin waka kwana 3 ya janye kalamansa ko ta kai shi kotu
- Kungiyar matan Kannywood wato K-WAN ta bukaci Naziru Sarkin waka ya yanke kalamansa kan matan masana'antar shirya fina-finan
- K-WAN ta ce ta ba mawakin kwanaki uku ya janye kalaman nasa ko kuma ya fuskanci fushin doka
- Tun farko dai Sarkin waka ya zargi wasu matan fim din da bayar da kansu ayi lalata da su domin a sanya su a cikin shirin fim
Kungiyar matan masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood wato K-WAN ta yi barazanar maka shahararren mawaki, Naziru Ahmad wato Sarkin waka a gaban kotun Musulunci.
K-WAN ta nemi Sarkin waka ya janye kazafin da ya yiwa matan masana'antar na cewa sai an yi lalata da wasun su kafin a sanya su a cikin shirin fim.
A wata sanarwa da shafin Kannywood ya wallafa a Facebook, kungiyar matan ta bashi tsawon kwanaki uku ya janye kalaman nasa daga ranar Litinin, 14 ga watan Fabrairu.
Sanarwar wacce ke dauke da sanya hannun shugabar kungiyar, Hauwa A Bello ta ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Assalamu alaikum. Kungiyar mata ta Kannywood Women Association Nigeria (K-WAN) karkashin jagorancin kungiyar Ni shugabar kungiya a madadin yan kungiya duba da abin da ya faru wanda Naziru M Ahmad ya yi wasu kalamai na cin zarafi ga mata masu sana'ar fim, muna kira gare shi da ya janye kalamansa cikin kwana uku daga yau in kuwa bai yi haka ba za mu maka shi a kotun Musulunci bisa zargin ya yi mana kazafi."
Naziru sarkin waka ya yiwa Ladin Cima da Fati Slow kyautan miliyoyin naira
A gefe guda, mun ji cewa mawakin Kannywood, Naziru Sarkin waka ya tare da yayyensa da ke masana'antar shirya fina-finan sun yi wa dattijuwar jaruma, Ladin Cima kyautar kudi naira miliyan biyu.
Naziru a cikin bidiyon da ya wallafa a shafinsa na Instagram, ya ce sun yi mata kyautar wannan kudi ne domin ta ja jari ta yadda za ta dunga samun na cin abinci. Ya kuma ce idan Allah ya barsu da rai za su dunga tallafa mata lokaci zuwa lokaci.
Hazalika ya ce an tura masa bidiyon abokiyar sana'arsa Fati Usman wacce aka fi sani da Fati Slow inda take ta raddi kan furucin da yayi a baya game da yadda ake lalata da mata a masana'antar.
Asali: Legit.ng