Kannywood: Rahama Sadau tana shirin sakin sabon fim mai dogon zango
- Fitacciyar jarumar Kannywood kuma furodusa, Rahama Sadau ta na shirin sakin sabon fim din ta mai dogon zango mai suna “Matar Aure”
- Fitacciyar jarumar ‘yar jihar Kaduna wacce ta samar wa kan ta suna a masana’antar ta sanar da sakin sabon fim din ta a shafin ta na Instagram
- A cikin fim din akwai manyan jarumai kamar Aminu Shariff, Yakubu Mohammed da sauran su kuma jarumar ce furodusar fim din kamar yadda ta bayyana
Shaharariyar jarumar masana’antar Kannywood, Rahama Sadau ta saki sabon fim din ta mai dogon zango mai suna “Matar Aure”, Daily Trust ta ruwaito.
Jarumar ‘yar asalin jihar Kaduna wacce ta samar wa kan ta suna a masana’antar Kannywood ta bayyana batun sakin fim din nata mai suna “Matar Aure” a shafin ta na Instagram.
A fim din manyan jarumai kamar Aminu Shariff, Yakubu Mohammed da sauran su sun taka rawa.
Ta ce nan kusa fim din zai fito
Jarumar ta sanar da batun sakin fim din nata wanda ita ce furodusa don Sadau Pictures ta shirya wanda tace nan ba da dadewa ba zai fito.
Hazikar jarumar ta shiga masana’antar a shekarar 2013 inda ta samu lambar yabo na jarumar da ta fi ko wacce kwarewa a masana’antar Kannywood a shekarar 2014 da 2015.
An taba dakatar da ita
Sai dai an dakatar da ita daga masana’antar a 2016 bayan ta bayyana a wani bidiyo tare da wani mawaki ‘Classique’ wanda aka ce ya ci karo da tarbiyya.
A shekarar 2018 aka dage dakatarwar da aka yi mata, wanda hakan ya janyo ta kara shahara inda ta fito a fina-finan Nollywood, MYV Shuga, fina-finai masu dogon zango da sauransu.
Na yi murabus daga ɗirka wa 'yan mata ciki, Mawaƙi 2Baba
A wani labarin, Shaharraen mawakin Najeriya da ya lashe kyaututuka da dama, Innocent Idibia da aka fi sani da 2Baba ya bayyana cewa ba zai sake yi wa wata mace ciki ba, The Nation ta ruwaito.
Mawakin, da ya yi wakar 'African Queen' ya bayyana hakan ne cikin wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta yayin bikin al'adu da kadade ta Idoma International Carnivial da aka yi a Otukpo, garinsu su 2Baba a Jihar Benue.
Asali: Legit.ng