Rashin Imani: Mahaifiya ta wanke ɗiyarta da tafasasshen ruwa kan aike

Rashin Imani: Mahaifiya ta wanke ɗiyarta da tafasasshen ruwa kan aike

  • Wata fusatacciyar matar aure a jihar Osun, Zainab, ta watsa wa diyar cikinta ruwan zafi a jiki saboda ta ƙi zuwa kai mata niƙa
  • Jami'an hukumar tsaro NSCDC reshen jihar sun yi ram da matar, wacce aka tabbatar ta aikata lamarin cikin fushi
  • Maƙociyar matar ta bayyana yadda matar ta aikata lamarin, tare da alƙawarin sai ta yi wa yarinyar dukan tsiya

Osun - Jami'an tsaro sun cafke wata mata mai suna, Zainab, dake zaune a yankin Oke Oniti, jihar Osun, bisa zargin watsa wa diyarta ruwan zafi.

Punch ta rahoto cewa matar ta wanke yarinyar yar kimanin shekara 11 a duniya da tafasasshen ruwa saboda taƙi zuwa aiken da ta mata.

Bayan faruwar lamarin, jami'an hukumar tsaro ta NSCDC, suka kame Zainab, kuma suka tsare ta a ofishin su kafin kammala bincike.

Kara karanta wannan

Mijina yana cizo na, ya lakaɗa mun duka idan ban yi abinci ba, Mata ta nemi kotu ta raba auren

Jihar Osun
Rashin Imani: Mahaifiya ta wanke ɗiyarta da tafasasshen ruwa kan aike Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Kakakin hukumar NSCDC reshen jihar, Daniel Adigun, a wata fira da ya yi ranar Talata, ya tabbatar da rahoton damƙe matar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tribune Online ta rahoto shi Ya ƙara da cewa:

"Matar tana cikin girki lokacin da abun ya faru. Ta illata ɗiyar da ruwan zafi saboda tana cikin fushi. A halin yanzu muna cigaba da bincike."

Yadda abun ya auku

Da take jawabin yadda lamarin ya faru, maƙociyar Zainab, wacce ta nemi a ɓoye sunanta, tace matar da aiki yarinyar ta kai mata niƙan Barkono, ita kuma taƙi zuwa.

"Cikin fushi, matar ta watsa wa yarinyar ruwan zafi har ta ji mata rauni. Nan take wata mata dake kusa da gidan ta shiga ta kwaci yarinyar zuwa waje."
"Maƙota ne suka kai yarinyar Asibiti kuma suka biya kuɗin kula da ita. Matar ta fito daga auren ta na farko inda ta haifi yarinyar, kafin ta aure mijinta na yanzu."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Mutane sun shiga daji sun kwato Sarkin su da yan bindiga suka sace a Filato

"A ranar da abun ya faru, yarinyar ta ɓatar da makullan gidan da suke zaune, daga baya ta ganshi, amma duk da haka matar tace sai ta yi mata duka, saboda haka take tsoron zuwa gidan."

A wani labarin na daban kuma Amarya da Ango sun rasa rayuwarsu lokaci daya makonni bayan baikon auren su

Wani saurayi da budurwarsa dake shirin zama Ango da Amarya sun rasa rayuwarsu lokaci ɗaya makonnin bayan amince wa zasu yi aure.

Masoyan biyu, Ma'aikatan jinya ne da suka yi aikin neman kwarewa a cibiyar lafiya ta tarayya dake jihar Adamawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags:
Online view pixel