Labaran duniya
An shiga jimamin rashin Sanata Doug Larsen mai wakiltar Dakota ta Arewa a majalisar dattawan Amurka bayan ya gamu da mummunan hatsarin jirgin sama.
Kamfanin WhatsApp zai dakatar da wasu manyan wayoyi daga amfani da manhajar a ranar Talata 24 ga watan Oktoba da mu ke ciki musamman masu girman 4.5.
Duniya da fadi yayin da wani matashi mai suna Sohib Ahmad ya siya wa budurwarsa makeken fili a duniyar wata mai girman eka daya don burge ta a Pakistan.
Sojojin mulkin Burkina Faso sun dakile yunkurin da wasu su ka yi na kifar da gwamnatin Kyaftin Ibrahim Traore a kasar bayan hawan shi mulki a shekarar 2022.
Kasar China ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga malamar Musulunci a yankin Uyghur marasa rinjaye a kasar kan zargin tayar da tarzoma da barazana ga tsaron kasar.
Shuaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya sha alwashin gyara kasar Najeriya ko da za a tsane shi a kasar, musamman wurin yakar talauci wanda shi ma ya taso a ciki.
Ghana ta kudiri aniyar taimakawa Najeriya da wutar lantarki bayan kasar ta fuskanci lalacewar wutar har sau biyu a cikin mako daya wanda ya yi sanadin daukewar wutar
Shugaban kasa, Bola Tinubu ya roki 'yan Najeriya da su dawo kasar saboda yanzu an samu sauyi ba kamar yadda su ka sani a da ba musamman harkokin tattalin arziki.
Hambararren shugaban kasar Nijar, Mohamed Bazoum ya maka sojin kasar a kotu don neman hakkinsa da aka tauye masa a matsayinsa na dan kasa da iyalansa.
Labaran duniya
Samu kari