Labaran duniya
Jawabin da aka samu daga ofishin mai magana da yawun bakin Bola Tinubu dabam da na UAE. Minista ya ce ba za a iya tsaida lokacin sake dawo da kamfanin jirage ba.
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna alhininsa bisa ibtila'in ambaliyar ruwan da ya afkawa ƙasar Libya, wacce ta yi sanadin rasuwar sama da mutane 6,000.
Wata mata ƴar ƙasar Kenya wacce ke rayuwa a kusa da rafin Baringo ta bayyana yadda kada ta raba ta da ƙafarta guda ɗaya. Ta ce rayuwa ta koma mai wuya a gareta.
A wani salo da ba a saba gani ba, kasar Faransa na rokon Morocco da ta yi hakuri ta karbi tallafin Yuro miliyan biyar da ta yi niyyar ba ta bayan girgizar kasa.
Yayin da ake ci gaba da zaman shiri tsakanin Jamhuriyar Nijar da kungiyar ECOWAS, sojin Nijar sun yanke alakar soji da kasar Jamhuriyyar Benin kan zargin zagon kasa.
Emmerson Mnangagwa ya gaji Robert Mugabe a 2017, har yanzu shi ne shugaban Zimbabwe. ‘Dan Shugaban Kasar ya zama Minista da Mahaifinsa ya sake darewa karagar mulki.
Wata mummunar ambaliyar ruwa da ta faru a ƙasar Libya ta yi sanadiyyar ɓacewar mutane aƙalla 10,000 tare da halaka wasu da dama. Lamarin ya faru ne a birnin Derna.
Wani mutumi mai shekara 50 a duniya wanda ya girgizar ƙasar Morocco ta ritsa da shi ya bayyana halin da ya tsinci kansa a ciki na zaɓin ceto iyayensa ko ɗansa.
Har yanzu ana ci gaba da aikin ceto nemo mutanen da girgizar ƙasar da ta auku a ƙasar Morocco ta rutsa da su. A yanzu haka an tabbatar da cewa mutane 2,497 ne.
Labaran duniya
Samu kari