Manyan Ƴan Siyasar Amurka 8 da ke Neman a Tsige Trump kan Yaƙi da Iran
A yayin da ake ƙoƙarin samun sulhu a kan rikicin Amurka da Iran, wasu fitattun ‘yan siyasa daga jam’iyyun Democrat da Republican sun fito suna sukar shugaban ƙasa, Donald Trump.
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
United States – Wasu manyan ƴan siyasa a Amurka sun fara kira da a tsige shugaban kasa Donald Trump ta hanyar amfani da sashe na 25 na kundin tsarin mulki.

Source: Facebook
Legit ta tattaro wasu daga cikin fitattun ‘yan siyasar da suka yi martani ga yakin da Trump ya jefa Amurka, tare buƙatar a tsige shi su huta.
Ƴan siyasa da ke neman a tsige Trump
1. Kamala Harris
Tsohuwar mataimakiyar shugaban ƙasa, Kamala Harris, ta yi kakkausar suka ga kalaman Trump, inda ta zarge shi da aikata laifuffukan yaƙi a shafinta na X.

Kara karanta wannan
DSS ta gano tsohon 'dan majalisa da ya kada hantar Amurka da rashin tsaro a Najeriya
Ta ce furucin da Trump ya yi na “shafe Iran” na nuna rashin tunani da rashin tsari a harkar shugabanci da ake fatan Amurka na da shi.

Source: Facebook
Harris ta jaddada cewa wannan mataki na iya jefa sojojin Amurka a cikin haɗari, musamman ganin cewa babu wata tabbatacciyar hanya ko tsari da aka gabatar na kawo ƙarshen rikicin.
2. Ilhan Omar
‘Yar majalisar dokoki daga Minnesota, Ilhan Omar, na daga cikin masu kira da a tsige Trump kai tsaye ba tare da an bata lokaci ba.
Ta bayyana kalaman da ya yi a matsayin tsantsar mugunta, musamman dangane da barazanar da ya yi wa Iran

Source: Twitter
A cikin saƙon da ta wallafa a shafin Facebook, Omar ta ce dole ne ‘yan jam’iyyar Republican su dauki mataki su cire Trump daga mulki idan ana son wanzar da zaman lafiya.
3. Bernie Sanders
Sanata Bernie Sanders shi ma ya yi tir da kalaman Trump, yana mai cewa abin takaici ne yadda shugaban ke barazanar kai hari ba tare da la’akari da illolin da hakan zai haifar ba.

Kara karanta wannan
2027: Matasa sun yi wa gidan tsohon shugaban kasa tsinke, ana so ya nemi kujerar Tinubu
Sanders ya bukaci ‘yan Republican su fito fili su yi magana, yana mai cewa lokaci ya yi da za a dakatar da Trump kafin lamarin ya wuce gona da iri.'

Source: Facebook
A cewarsa, dole ne a kawo ƙarshen wannan rikici cikin gaggawa domin kauce wa fadawa cikin wani babban yaƙi da ka iya zama na duniya baki ɗaya.
4. Tim Walz
Gwamnan Minnesota, Tim Walz, ya bayyana cewa shugaban ƙasa Trump ba ya cikin yanayi na hankali wajen yanke irin waɗannan hukunci.
Walz ya bayyana cewa kalaman Trump sun nuna rashin daidaiton tunani, musamman a lokacin da ake bukatar shugabanci mai natsuwa, kamar yadda International Business Times ta wallafa.

Source: Getty Images
Walz ya nuna damuwa cewa irin waɗannan furuci na iya tayar da hankula a duniya tare da ƙara dagula al’amura maimakon samar da mafita.
5. Hakeem Jeffries
Shugaban marasa rinjaye a majalisar dokoki, Hakeem Jeffries, ya yi kira ga ‘yan majalisa da su dauki mataki cikin gaggawa don dakatar da rikicin.
Jeffries ya gargadi cewa idan ba a yi sauri ba, Trump na iya jefa Amurka cikin yaƙin duniya na uku, wanda zai haifar da babbar asara ga duniya baki ɗaya.

Source: Facebook
Ya kuma bukaci ‘yan Republican su fifita kishin ƙasa a kan siyasar jam’iyya, yana mai cewa lokaci ya yi da za a dakatar da abin da ya kira mahaukaciyar siyasa.
6. Amy Klobuchar
Sanata Amy Klobuchar ta bayyana barazanar Trump a matsayin rashin hankali, tana mai cewa irin wannan magana ba ta dace da shugaban ƙasa ba.
Ta bukaci majalisa ta gaggauta kada kuri’a domin dakatar da duk wani mataki da zai iya haifar da tashin hankali a Iran, kamar yadda BBC Hausa ta wallafa.
A ganinta, wannan lamari na bukatar daukar mataki cikin gaggawa kafin ya rikide zuwa wani babban rikici.
7. Lisa Murkowski
Sanata Lisa Murkowski ta bayyana cewa babu wani uzuri da zai sa a amince da barazanar Trump a matsayin hanyar tattaunawa da Iran.
Ta nuna cewa irin wannan lamari bai dace da ƙa’idodin diflomasiyya ba, kuma tana iya lalata dangantaka tsakanin ƙasashe, kamar yadda CNBC ta wallafa.
Murkowski ta kuma nuna damuwa cewa Amurka na iya rasa martabarta a idon duniya idan ta ci gaba da irin wannan salon siyasa.
8. Yassamin Ansaru
Yassamin Ansari, yar majalisar wakilan Amurka mai asalin Iran, ta caccaki Donald Trump kan kalamansa game da Iran, inda ta ce yana kokarin zama sarki mai mulkin mallaka maimakon shugaba.

Source: Twitter
Ansari ta bayyana cewa kalaman Trump na barazana ga Iran na iya jefa rayuwar mutane kusan miliyan 90 cikin hadari.
Ta ce irin wadannan furuci na nuna rashin kula da rayukan fararen hula da kuma rashin ingantaccen shugabanci, inda ta buƙaci a tsige shi don samun zaman lafiya.
Trump ya gargaɗi Netanyahu
A baya, mun wallafa cewa Amurka ta yi gaggawar gargadin Benjamin Netanyahu kan hare-haren Isra’ila a Lebanon domin kar ya rusa sharadin tsagaitawa da aka yi da Iran.
Shugaba Donald Trump ya bukaci Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu da ya rage yawan hare-haren da ke barazana ga tsagaita wutar yayin da ake shirin fara tattaunawa.
Hakan na zuwa ne bayan Isra’ila ta ce za ta fara tattaunawa da Lebanon bayan Trump ya aika da saƙo mai ƙarfi ga Netanyahu ta wayar tarho a kan hare-haren.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

