Yadda Iran Ta Riƙa Kakkaɓo Jiragen 'Maƙiya' daga Sararin Samaniyarta
- Iran ta ce ta kakkabo jiragen sama marasa matuƙa da abokan gaba suka rika aika mata domin a kai hare-hare
- Sojojin ƙasar ta Iran sun ce sun shirya dakile jiragen yaƙi da marasa matuƙa da da sababbin kayan aiki da suka samar a cikin gida
- Rahotanni na cewa dabarun yaƙin Iran da sababbin fasahohin da ake amfani da su sun jefa abokan gaba cikin ruɗani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Iran – Ƙasar Iran ta bayyana cewa dakarunta sun samu nasarar kakkabo sama da jiragen sama marasa matuƙa 160 na abokan gaba, a wani sabon bayani da ya fito daga rundunar tsaron sararin samaniyarta.
Kwamandan hedikwatar haɗin gwiwar tsaron sararin samaniya na ƙasar, Birgediya Janar Alireza Elhami ne ya bayar da tabbacin.

Source: Twitter
Al-Jazeera ta wallafa cewa Birgediya Janar Alireza Elhami ya ce sojojin Iran sun riga sun lalata jiragen yaƙi masu ƙarfi da dama a hare-haren da aka kai wa ƙasarsa.
Iran ta kakkaɓo jiragen abokan gaba
Financial Express ta wallafa cewa Birgediya Janar Alireza Elhami ya ce dimbin makamai masu linzami na 'cruise', da kuma jirage da dama marasa matuƙada suka haɗa da nau’uikan 'Hermes' da 'Lucas'.
A cewarsa, wannan nasara ta samu ne sakamakon sababbin dabaru da kuma amfani da ingantattun kayan aikin tsaro da aka ƙera a cikin ƙasarta.
Sanarwar ta ƙara da bayyana cewa rundunar tsaron sararin samaniyar Iran na ci gaba da ƙarfafa matakan kare ƙasar daga hare-haren sama da Isra'ila da Amurka ke kai mata.
Sojojin Iran sun shirya kare ƙasarsu
Janar Elhami ya ƙara da cewa sojojin Iran a shirye suke su kai farmaki ko su yi kwanton ɓauna ga jiragen yaƙin abokan gaba da kuma jiragen marasa matuƙa, ta amfani da hanyoyi na zamani.
Haka kuma ana shirya za a yi amfani da kayan aiki na cikin gida da aka ƙera domin farautar jiragen zamani na ƙarni na biyar da kuma sababbin jiragen marasa matuka .
Ya bayyana cewa:
“Sojojinmu a shirye suke su yi kwanton ɓauna ga jiragen yaƙi da marasa matuƙa na abokan gaba ta amfani da hanyoyi da kayan aiki na zamani da aka ƙera a cikin gida domin yaƙar jiragen ƙarni na biyar da kuma na’urorin jirage marasa matuƙa na zamani.”

Source: Getty Images
Ya ƙara da cewa:
"Mun riga mun lalata jiragen yaƙi masu ƙarfi da dama, tare da makamai masu linzami da dama."
A cewarsa, wannan nasara ta samo asali ne daga dabaru da kuma amfani da sababbin kayan aiki da kirkire-kirkire a tsarin tsaro, wanda ya ce ya jefa abokan gaba cikin ruɗani da rashin fahimta.
Kalaman na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun tashin hankali a yankin, inda ƙasashe ke ƙara ƙarfafa tsaronsu na sararin samaniya da kuma fasahohin yaƙi na zamani.
Iran ta yi magana kan sulhu
A baya, kun ji cewa Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya ce ana jirkitar da matsayinsu kan batun sulhu a yaƙin da ake gwabzawa a kafafen yada labaran Amurka.
Abbas Araghchi ya kuma jaddada cewa kasar Iran na son sharuddan da za su kawo ƙarshen yaƙi gaba ɗaya ne, ba wai a ɗan tsagaita na wani takaitaccen lokaci ba.
Ya gode wa Pakistan kan ƙoƙarin sasanci, yana mai cewa ba su taɓa ƙin ziyartar Islamabad ba a kan maganar sulhu a yaƙin da ake yi a Gabas ta Tsakiya ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


