Iran Ta Harbo Jirgin Yaƙin Amurka, An Sanya Ladar Kudi ga Wanda Ya Kamo Matuƙan

Iran Ta Harbo Jirgin Yaƙin Amurka, An Sanya Ladar Kudi ga Wanda Ya Kamo Matuƙan

  • Rundunar sojin Amurka da ta Isra'ila sun tabbatar da cewa Iran ta harbo wani jirgin yaƙin Amurka a sararin samaniyarta a yau Juma'a
  • Rahoto ya nuna cewa Amurka ta tura dakarun ceto na musamman domin gano matuƙan jirgin kafin dakarun Iran su yi awon gaba da su
  • A hannu daya, ita kuma Iran ta sanya lada mai tsoka ga duk wanda ya bada bayanin ko ya kamo wadannan matuka da suka fada kasar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Iran – Gabas ta Tsakiya ta ƙara rikicewa a yau Juma'a, 3 ga Afrilu, 2026, bayan dakarun ƙasar Iran sun samu nasarar kakkabo wani jirgin yaƙin Amurka dake shawagi a sararin samaniyar ƙasar.

Wannan lamari ne da ya jefa dakarun Amurka dake yankin cikin shirin ko-ta-kwana domin ceto matuƙan jirgin da har yanzu ba a san halin da suke ciki ba yau.

Kara karanta wannan

Ko ina ya kama da wuta: An gano ɓarnar da Iran ta yi wa Kuwait, ƙawar Amurka

Iran ta harbo wani jirgin yakin Amurka
Makami mai linzami da Iran ta harba (hagu) da jirgin yakin kasar Amurka (dama). Hoto: Kevin C. Cox and Mostafa Alkharouf/Anadolu via Getty
Source: Getty Images

Ana neman matukan jirgin da Iran ta harbo

Rahotanni daga majiyoyin soja daban-daban sun nuna cewa Amurka ta baza jirage marasa matuka da kuma jirgin nan mai dakon kaya na Hercules C-130 domin laluben inda jirgin ya faɗi, in ji rahoton New York Times.

Sai dai wannan aiki yana fuskantar gagarumin ƙalubale domin dakarun Iran sun nuna shirye-shiryensu na harbo kowane irin jirgi dake ƙoƙarin shiga yankin.

Kamfanin dillacin labarai na Tasnim ya ruwaito cewa wani jirgi mai saukar ungulu na Amurka ya tsallake rijiya da baya bayan da ya fuskanci harin dakarun Iran a aikin ceton da yake yi.

Haka kuma, kafofin yaɗa labarai dake da alaƙa da sashen shari'ar Iran, sun wallafa hotunan suka ce na jiragen Amurka ne dake shawagi a sararin samaniyar ƙasar.

A ɓangare ɗaya, gidan talabijin na Gwamnatin Iran ya yi kira ga mazauna yankin da su kamo "matuƙan jirgin maƙiyan" su miƙa su ga jami'an tsaro domin samun gagarumar kyauta.

Kara karanta wannan

Iran ta harbo hatsabibin jirgin Amurka daga sama, ya fado kasa ya wargaje

Dalilin fusatar dakarun kasar Iran

Harin kakkabo jirgin ya faru ne sa'o'i kaɗan bayan da Shugaba Donald Trump ya wallafa a shafukan sada zumunta cewa dakarun Amurka sun yi nasarar lalata gadar B1 dake tsakanin Tehran da gaɓar tekun Caspian.

Shugaban ya yi murnar wannan nasara tare da yin gargaɗin cewa "akwai sauran wasu hare-haren dake tafe," kamar yadda rahoton BBC ya nuna.

Majiyar sojin Amurka ta bayyana cewa sun harbi gadar ne har sau biyu domin toshe hanyar da Iran ke amfani da ita wajen kai wa dakarunta na makaman linzami da na jirage marasa matuƙi (drones) kayayyaki.

Amurka ta tura jirage don nemo matukan jirgin yakinta da Iran ta kakkabo.
Dakarun sojojin Amurka na bataliyar USMC sun isa sansanin horo na UWTCa Kudancin Isra'ila. Hoto: JACK GUEZ/AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Sojojin Amurka na shirin ko-ta-kwana

Rahotanni daga Iran sun tabbatar da cewa harin gadar ya yi sanadiyyar mutuwar mutane takwas yayin da wasu 95 suka ji rauni yau.

Wannan gagarumin takun-saƙa tsakanin manyan ƙasashe biyu ya nuna cewa yaƙin yankin ya kai wani mataki mai ban tsoro.

A halin yanzu, dakarun Amurka dake ƙasashen Iraƙi da Siriya suna cikin shirin kowace irin fito-na-fito yayin da ake ci gaba da neman matuƙan jirgin a cikin daji da duwatsun ƙasar Iran.

Kara karanta wannan

Yemen ta shiga yakin Iran gadan gadan, ta harba makami mai linzami zuwa Isra'ila

Kasar Iran ta harbo jirgin Amurka

A wani labarin, mun ruwaito cewa, dakarun IRGC na kasar Iran sun yi nasarar harbo wani jirgin sojojin Amurka samfurin F-35 daga sama.

Hakan na zuwa ne bayan barazanar da Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi kan cewa zai cigaba da lalata muhimman wurare a Iran.

A daya bangaren, an samu rahotanni da suka nuna cewa an ka hari da jirgi maras matuki wata matatar mai da ke yankin Al Ahmad na Kuwait.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com