Rashin Taya Trump Yaki da Iran Ya Harzuƙa Shi, Ya Ci Mutuncin Shugaban Faransa da Matarsa

Rashin Taya Trump Yaki da Iran Ya Harzuƙa Shi, Ya Ci Mutuncin Shugaban Faransa da Matarsa

  • Kalaman Donald Trump da ya yi wa Emmanuel Macron da matarsa Brigitte Macron sun tayar da kura a kasar Faransa
  • ‘Yan siyasa ciki har da masu adawa da Macron sun fito sun kare shi, suna cewa kalaman Trump rashin mutunci ne duk da bambancin ra’ayi a tsakaninsu
  • Macron ya ce kalaman Trump ba su da kima kuma ba su dace ba, yayin da rikicin Iran ke gudana yana bukatar hankali ba zolaya ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Shugaban Amurka Donald Trump ya haddasa ce-ce-ku-ce a Faransa bayan ya yi wa shugaban kasar Emmanuel Macron da matarsa Brigitte Macron ba’a.

Rahotanni sun ce Trump ya kwaikwayi lafazin Faransanci yana cewa matar Macron tana wulakanta shi, lamarin da ya fusata ‘yan siyasa da dama a kasar Faransa.

Kara karanta wannan

Rigima sabuwa: Trump ya jefawa mataimakinsa zargi kan yakin Iran

Trump ya tayar da bayan cin mutuncin Macron da matarsa
Shugaba Donald Trump na Amurka da Emmanuel Macron na Faransa. Hoto: Picture alliance.
Source: Getty Images

Wannan magana ta zo ne yayin da Trump ke sukar kawayen NATO saboda kin shiga yakin Iran, yana mai cewa sun gaza bayar da taimako da ake bukata, cewar France 24.

Yadda aka caccaki Trump kan sukar Macron

A Faransa, ‘yan siyasa ciki har da Shugaban majalisar wakilai Yaël Braun-Pivet sun ce kalaman ba su dace ba kuma sun saba da mutunci na shugabanci.

Ta bayyana cewa duniya na cikin mawuyacin hali musamman a Iran inda rayuka ke salwanta, don haka bai dace shugaba ya rika yin ba’a ba.

Ko da Manuel Bompard wanda ke adawa da Macron ya ce duk da sabani tsakaninsu, kalaman Trump sun wuce gona da iri kuma ba za a amince da su ba.

Shugaba Macron da yake ziyara a Koriya ta Kudu ya ce kalaman Trump ba su da kima kuma ba su dace da matsayin shugabanci ba.

An caccaki Trump a Faransa kan sukar shugaba Macron
Shugaba Donald Trump yana jawabi a birnin Washington. Hoto: Al Drago/Bloomberg.
Source: Getty Images

Trump ya tuno tsohon bidiyon Macron da matarsa

Kara karanta wannan

Trump ya gindaya sharudan tsagaita wuta, ya fadi rokon da Iran ta yi masa

Trump ya kuma ambaci wani tsohon bidiyo da aka dauka a 2025 inda aka zargi matarsa da ture shi, amma Macron ya ce wannan wasa ne ba rikici ba.

Macron ya jaddada cewa babu wata matsalar aure tsakaninsa da matarsa, yana mai cewa suna wasa ne kamar yadda suka saba yi a kullum, cewar Independent TV.

A jawabinsa, Trump ya ce ya nemi Faransa ta tura jiragen ruwa domin taimako a yankin Gulf amma Macron ya ki amincewa a lokacin yakin.

Trump ya kuma yi kwaikwayon yadda Macron ya amsa masa cikin lafazin Faransanci, yana mai cewa za su iya taimakawa ne bayan an kammala yaki.

A karshe, Trump ya soki NATO yana kiranta kungiyar marar karfi, yana mai cewa ba za ta taimaka ba idan aka fuskanci babban rikici a gaba.

Trump ya gindaya sharuda ga kasar Iran

A wani labarin, an ji cewa Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi magana game da yunkurin tsagaita wuta da Iran ta nema a yi a yaƙin da ake yi.

Trump ya ce Shugaban Iran yana neman tsagaita wuta, duk da sabanin kalamansa kan dakatar da yakin ko kara tsananta shi.

Iran ta ci gaba da kai hare-hare a yankin Tekun Fasha, yayin da farashin mai ya tashi sakamakon rikicin da ya shafi mashigar Hormuz.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.