Yayin da Ta Ke Tsaka da Yaki da Iran, Isra’ila Ta Fadi Kasar da Za Ta Mamaye

Yayin da Ta Ke Tsaka da Yaki da Iran, Isra’ila Ta Fadi Kasar da Za Ta Mamaye

  • Ministan tsaron Israa, Israel Katz ya yi magana kan shirin da Isra’ila ke yi na mamaye wasu yankunan kudancin Lebanon
  • Katz ya bayyana kudirin kafa yankin tsaro har zuwa kogin Litani tare da ci gaba da ikon tsaro domin fadada ikonta
  • Ya ce za a hana mazauna yankin dawowa, tare da rusa gidaje kamar yadda aka yi a Gaza wanda ya jawo magana

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tel Aviv, Israel - Ministan tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya yi magana game da ci gaba da yaki a Gabas ta Tsakiya.

Katz ya bayyana cewa sojojin kasar na shirin mamaye wasu yankunan kudancin Lebanon ko bayan kammala yakin da suke yi da kungiyar Hezbollah.

Isra'ila za ta mamaye Lebanon
Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu yayin jawabi a Tel Aviv. Hoto: Benjamin Netanyahu.
Source: Facebook

A cikin wani bidiyo da ya fitar wanda Al Jazeera ta samu, Katz ya bayyana cewa ana shirin kafa wani yankin tsaro na dindindin a cikin kasar Lebanon, wanda zai kai har zuwa kogin Litani.

Kara karanta wannan

Abu ya gagara: Trump zai janye yaki da Iran ba tare da cika wani burinsa ba

Asarar da aka yi a yakin Iran/Isra'ila

Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da yakin kasar Iran da Isra'ila tare da goyon bayan Amurka karkashin Donald Trump.

A ranar 28 ga watan Fabrairun shekarar 2026 Isra'ila da Amurka suka kai hari a birnin Tehran wanda ya yi barna da jawo asarar rayuka.

Harin ya yi sanadiyyar mutuwar jagoran addini a Iran, Ayatollah Ali Khamenei da wasu manyan jami'an tsaron kasar.

Daga bisani, Iran ta mayar da martani mai zafi inda ta lahanta Isra'ila da Amurka wanda har yanzu ake ci gaba da yaki.

Bayan yakin Iran, Isra'ila za ta mamaye Lebanon
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu da sabon jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei. Hoto: Gil Cohen-Magen.
Source: Getty Images

Abin da sojojin Isra'ila ke shirin yi

Katz ya ce sojojin kasar Isra'ila za su kafa sansanin tsaro a cikin wasu yankunan Lebanon domin karfafa ikon tsaro a wurin.

Ya ce:

“A karshen wannan aiki, rundunar sojin Isra’ila za ta kafa kanta a yankin tsaro a cikin Lebanon, kuma za ta ci gaba da rike ikon tsaro a duk yankin har zuwa kogin Litani.”

Kara karanta wannan

APC tana cikin matsala, maganar tikitin Kwankwaso da Obi ya fara jan hankali

Ministan ya kuma ce za a hana mazauna Lebanon da aka raba da muhallansu komawa yankunansu bayan yaki, cewar Times of Israel.

Ya kara da cewa za a aiwatar da irin tsarin da aka yi a Gaza, inda aka rusa gidaje a yankunan kan iyaka.

“A dukkan gidajen da ke kauyukan da ke kusa da iyaka a Lebanon za a rushe su bisa tsarin da aka yi a Rafah da Beit Hanoon a Gaza."

- Israel Katz

Yakin Iran: Fafaroma ya shawarci Isra'ila da Amurka

Tun farko, kun ji cewa Shugaban darikar Katolika na duniya, Fafaroma Leo XIV ya yi sake yin magana game da yakin Iran da Isra'ila a Gabas ta Tsakiya.

Fafaroma ya ce Allah ba ya karɓar addu’o’in shugabannin da ke tayar da yaƙe-yaƙe, yana mai cewa hannayensu sun cika da jini.

Yayin bikin Palm Sunday, ya ce Yesu mai son zaman lafiya ne, kuma ba za a yi amfani da shi wajen halatta yaƙi ba inda ya tabbatar da matsalar da ke tattare da haka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.