Amurka da Isra'ila Sun Sake Tafka Babbar Asara a Yaki da Iran da Aka Kakkabo Jirgin MQ 9

Amurka da Isra'ila Sun Sake Tafka Babbar Asara a Yaki da Iran da Aka Kakkabo Jirgin MQ 9

  • Dakarun sojojin kasar Iran sun yi ikirarin kakkabo jirgin leken asiri kirar MQ-9 Reaper, wanda darajarsa ta kai Dala miliyan 30
  • Rahotanni sun nuna cewa jirgin MQ-9 Reaper na daga cikin manyan jiragen leken asiri da ake amfani da su wajen kai hare-hare da tattara bayanai
  • Sojojin Iran sun ce wannan jirgi shi ne na 146 da suka harbo tun bayan barkewar yaki tsakanin Jamhuriyar Musulunci da kasashen Amurka da Isra'ila

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Iran - Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sake yi wa Amurka/Isra'ila barna yayin da kasashen ke ci gaba da musayar wuta a tsakaninsu.

Rundunar sojin Iran ta sanar da cewa ta harbo wani jirgin yaki marar matuki (drone) kirar MQ-9 a kusa da birnin Isfahan, tana mai cewa jirgin na “makiyanta Amurka da Isra’ila” ne.

Kara karanta wannan

Kasar Iran ta illata Isra'ila, ta babbake wani babban kamfani a farmakin da ta kai

MQ-9 Reaper.
Jirgin leken asiri kirar MQ-9 Reaper na kasar Amurka Hoto: Miguel J. Rodriguez
Source: Getty Images

Iran ta kakkabo jirgin MQ-9 Reaper

A cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya wallafa, jami’an hulda da jama’a na sojojin Iran sun ce an gano jirgin tare da kakkabo shi a ranar Talata.

Jirgin MQ-9 Reaper na daga cikin manyan jiragen leken asiri da ake amfani da su wajen kai hare-hare da tattara bayanai, kuma darajarsa na kai kusan Dala miliyan 30 kowanne.

Jiragen da Iran ta harbo a yaki da Amurka

Sojojin Iran sun ce wannan jirgi shi ne na 146 da suka harbo tun bayan barkewar yaki tsakanin Jamhuriyar Musulunci da hadakar Amurka da Isra'ila a ranar Asabar 28 ga watan Maris, 2026.

Wannan ya kara nuna yadda ake gwabza azababben yaki tsakanin kasasshen ta hanyar harba jirage marasa matuka da makamai masu linzami, cewar rahoton Al-Jazeera.

Sanarwar kakkabo jirgin da sojojin Iran suka fitar na kara nuna yadda rikicin tsakanin kasar da kasashen Amurka da Isra’ila ke kara tsananta, musamman ta fuskar hare-haren jiragen sama marasa matuka.

Kara karanta wannan

Yaki ya yi zafi; Iran ta farmaki sojojin Amurka 500, an ji abin da ya faru

Shin akwai alamun tsagaita wuta?

Yakin, wanda aka fara a ranar Asabar 28 ga watan Maris, 2026, na ci gaba da jawo asarar rayuka da dukiyoyi a kowane bangare, lamarin da ya zama barazana ga tsaro musamman a yankin Gabas ta Tsakiya.

Har yanzu dai babu alamun dakatar da wannan yaki duk da Amurka ta yi ikirarin cewa sun fara tattaunawa da Iran domin tsagaita wuta.

A nata bangaren, Iran ta fito ta karyata wannan ikirari a lokuta daban-daban amma daga baya ta ce wasu kasashe da dama sun fada mata Amurka na son kawo karshen wannan yaki ta hanyar tattaunawa.

Spain ta hana Amurka amfani da iyakokinta

A wani labarin, kun ji cewa kasar Spain ta hana jiragen yakin Amurka amfani da sararin samaniyarta yayin da ake ci gaba da musayar wuta a yankin Gabas ta Tsakiya.

Wannan matakin da Spain ta dauka ya shafi yakin da hadin guiwar Amurka da Isra'ila ke yi da Iran, wanda aka fara a karshen watan Fabrairun 2026.

Ministar tsaron kasar, Margarita Robles, ta bayyana cewa gwamnatin Spain ba za ta amince da amfani da sararin samaniyarta ko sansanonin soji ba domin ayyukan da suka shafi yakin Iran.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262