Sojojin Isra'ila Sun Sha Wuta a Hannun Hezbollah, an Tura da Dama Barzahu

Sojojin Isra'ila Sun Sha Wuta a Hannun Hezbollah, an Tura da Dama Barzahu

  • Mayakan Hezbollah na ci gaba da fafatawa da sojojin Isra'ila wadanda suka yi kutse zuwa Kudancin Lebanon a yankin Gabas ta Tsakiya
  • A wata sabuwar arangama da aka yi, mayakan na Hezbollah sun samu nasarar hallaka wasu daga cikin sojojin Isra'ila
  • Rundunar sojojin Isra'ila (IDF) ta tabbatar da cewa an hallaka jami'anta, inda ta fitar da sunayen wadanda aka tura barzahu

​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Tel-Aviv, Isra'ila - Rundunar sojojin Isra'ila (IDF) ta sanar da cewa mayakan kungiyar Hezbollah sun hallaka sojojinta a Lebanon.

Rundunar IDF ta bayyana cewa an kashe sojojinta hudu yayin da wasu biyu kuma suka jikkata a wata fafatawa da mayakan Hezbollah a Kudancin Lebanon a ranar Litinin, 30 ga watan Maris 2026.

Hezbollah ta kashe sojojin Isra'ila
Wasu daga cikin sojojin kasar Isra'ila Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Mai magana da yawun bakin rundunar IDF, Birgediya Janar Effie Defrin, ya bayyana hakan a shafinsa na X a ranar Talata, 31 ga watan Maris 2026.

Kara karanta wannan

Sojojin Isra'ila sun sha kashi, mayakan Hezbollah sun samu nasara a kansu

Sojojin Isra'ila da Hezbollah ta kashe

Birgediya Janar Effie Defrin ya bayyana cewa waɗanda suka mutun sun haɗa da sojoji biyu ’yan shekara 21, soja guda ɗan shekara 22, da kuma soja na huɗu wanda ba a bayyana bayanansa ba saboda "ba a riga an amince da wallafa sunansa ba."

An bayyana sunayen sojoji uku daga cikin waɗanda aka kashe kamar haka:

  • Kyaftin Noam Madmoni, ɗan shekara 22, daga Sderot.
  • Sajan Ben Cohen, ɗan shekara 21, daga Lehavim.
  • Sajan Maxsim Entis, ɗan shekara 21, daga Bat Yam.

An raunata wasu sojojin

Dukkansu sun yi aiki ne a sashen bincike na rundunar Nahal Brigade. Rundunar ta ce za a bayyana sunan soja na huɗu nan gaba.

Bugu da ƙari, soja ɗaya ya ji rauni mai tsanani, yayin da wani sojan daban ya ji rauni matsakaici a yayin lamarin.

IDF ta gudanar da bincike

A cewar binciken da rundunar IDF ta gudanar kan lamarin, lokacin gudanar da ayyuka a sashen yammacin Kudancin Lebanon da misalin ƙarfe 6:30 na yammacin jiya, dakarun sashin bincike na Nahal sun hango wasu rukunin mayakan Hezbollah ɗauke da makamai.

Kara karanta wannan

Sojojin Isra'ila sun sha azaba a hannun mayakan Hezbollah, an ji abin da ya faru

Rahoton jaridar The Times of Israel ya ce binciken sojojin ya nuna cewa sojojin sun yi musayar wuta da mayakan na Hezbollah daga nesa kaɗan, inda suka harbi da dama daga cikinsu.

Mayakan Hezbollah sun kashe sojojin Isra'ila
Sojan Isra'ila da mayakan Hezbollah suka kashe Hoto: @IDFSpokesperson
Source: Twitter

Hezbollah na fafatawa da sojojin Isra'ila

Yayin da ake ƙoƙarin kwashe sojojin da suka ji rauni daga wurin fafatawar, mayakan Hezbollah sun harba makamin fasa tankoki ga dakarun, wanda binciken ya ce bai janyo ƙarin wasu raunuka ba.

Rundunar IDF ta ce ta mayar da martani ta hanyar yin luguden wuta da tankokin yaƙi da hare-haren sama kan mayakan Hezbollah da ke yankin.

Aƙalla sojojin Isra'ila 10 ne aka kashe a Kudancin Lebanon tun daga ranar 2 ga Maris yayin da Isra'ila ke faɗaɗa mamayarta a ƙasar.

Iran ta kai hari kan Israila

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar IRGC ta kasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kai sababbin hare-hare kan muhimman wurare na Amurka da Isra'ila.

​Rundunar IRGC ta ce ta farmaki cibiyoyin kula da yaki Amurka da Isra'ila, wuraren ajiye jirage marasa matuƙa da maboyar matuƙan jirgi a sababbin hare-haren.

IRGC ta ce ta farmaki wuraren ne ta hanyar amfani da makamai masu linzami masu dogon zango a matsayin ɓangare na jerin hare-hare na 87 na samamen Operation True Promise 4.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng