Iran Ta Sake Illata Amurka da Isra’ila bayan Jefa Bama Bamai da Suka Yi

Iran Ta Sake Illata Amurka da Isra’ila bayan Jefa Bama Bamai da Suka Yi

  • Rundunar tsaro ta IRGC da ke kasar Iran ta bayyana nasarar da ta samu yayin da ake ci gaba da yaki a Gabs ta Tsakiya
  • IRGC ta ce ta lalata bama-bamai 120 a yankin Fars wadanda aka jefa yayin hare-haren Amurka da Isra’ila kwanaki da suka gabata
  • Rahoto ya ce an gano su a kauyen Kafri da wasu yankuna da ke kusa dauke da bama-baman wadanda ke da mugun hatsari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Fars, Iran - Rundunar 'Islamic Revolutionary Guard Corps' watau IRGC ta Iran ta bayyana nasarar da ta samu kan Amurka da Isra'ila.

IRGC ta bayyana cewa ta gano tare da lalata bama-bamai masu yawa guda 120 a lardin Fars da ke kudancin kasar.

Iran ta lalata bama-baman Amurka da Isra'ila
Jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei da Shugaba Donald Trump na Amurka. Hoto: Imam Mojtaba Khamenei, Donald J Trump.
Source: Facebook

A cewar rundunar, an jefa wadannan makamai ne a yayin hare-haren hadin gwiwa na Amurka da Isra’ila da aka kai kwanaki da suka gabata, cewar Al Jazeera.

Kara karanta wannan

Iran ta gano masu ba sojojin Amurka mafaka, ta sha alwashin ruguza su da hare hare

Gargadin da Iran ta yi kasashe makwabtanta

Wannan nasara ta Iran na zuwa ne bayan gargadi da ta aika ga kasashe makwabtanta kan ba sojojin Amurka wurin zama musamman a otal otal.

Kasar ta yi gargadi mai tsauri ga wasu mamallakan otal otal a yankin da take gwabza yaki da Isra'ila a yankin Gabas ta Tsakiya.

Ta ce duk wasuotal da ke daukar sojojin Amurka a yankin za su zama halastattun wuraren kai hare-hare yayin rikicin da ke gudana.

Kakakin rundunar Iran ya ce idan sojojin kasar Amurka suka fake a otal, hakan na nufin wurin ya zama makasudin kai hari kai tsaye.

An lalata bama-baman Amurka da Isra'ila a Iran
Jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei, Shugaba Donald Trump na Amurka da Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu. Hoto: Imam Mojtaba Khamenei, Donald J Trump, Benjamin Netanyahu.
Source: Facebook

Iran ta yi nasarar tarwatsa bama-baman Amurka

Rahotanni sun ruwaito cewa mataimakin shugaban hulda da jama’a na rundunar IRGC a Fars yana bayyana cewa an gano bama-baman ne a kauyen Kafri da wasu yankunan da ke kusa.

Ya ce matakin ya gano da lalata wadannan bama-bamai ya taimaka wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma daga hadarin fashewa.

Kara karanta wannan

Iran ta yi babban kamu, an gano mutane da ke yada sirrinta ga makiya a yaki da Isra'ila

Hukumomin sun kara da cewa ana ci gaba da bincike a yankunan domin gano duk wasu makamai da ba su fashe ba.

Sun jaddada cewa rundunar na daukar matakai domin tabbatar da tsaro da kare fararen hula daga illolin yakin da ake ciki, kamar yadda WANA News Agency ta ruwaito.

Iran na ci gaba da kai hare-hare kan Amurka da Isra'ila tun bayan harin da suka kai wanda ya yi sanadiyyar Ayatollah Ali Khamenei.

An cafke masu leken asiri a kasar Iran

A baya, kun ji cewa hukumomin Iran na ci gaba da samun galaba kan Isra'ila da Amurka a yakin da suke yi da ƙasar Isra'ila a yankin Gabas ta Tsakiya.

Ƙasar ta cafke wasu mutane akalla 15 a Isfahan bisa zargin aika muhimman bayanai zuwa kafafen yada labarai da ta ke yi wa kallon makiya.

Rahotanni sun ce ana zargin wadanda aka kama da bayyana wuraren sojoji da kuma hotunan barnar hare-hare ga wasu hanyoyin sadarwa na waje.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.