"Kada Ku ba Makiya Dama": Iran Ta Sabunta Gargaɗi ga Ƙasashen Gabas Ta Tsakiya

"Kada Ku ba Makiya Dama": Iran Ta Sabunta Gargaɗi ga Ƙasashen Gabas Ta Tsakiya

  • Iran ta jaddada cewa ba ta taɓa kai hari da farko, amma wannan ba ya nufin za ta ɗauki zaluncin kawo mata hari har gida
  • Shugaban kasar, Masoud Pezeshkian ne ya bayyana haka a yayin da ƙasarsa ke ci gaba da mayar da martani mai zafi a yaƙin Gabas ta Tsakiya
  • Ya gargadi ƙasashen yankin da kada su bari a yi amfani da ƙasashensu wajen kai hari Iran, saboda hakan na nufin za su yi ramuwar gayya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Ƙasar Iran –Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya sake nanata matsayar ƙasarsa a kan batun tsaro da martani ga duk wata barazana daga ƙasashen waje.

Yakin da Amurka da Isra'ila suka tsira da Iran na ci gaba da daukar zafi tare da dagula tattalin arzikin duniya, musamman ta fuskar man fetur.

Kara karanta wannan

Pakistan ta gana da Iran, an taɓo batun sulhu da Amurka

Iran ta sake tura gargadi ga ƙasashen Gabas ta Tsakiya
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian yana gyara abin kunne a wani taro Hoto: Masoud Pezeshkian
Source: Getty Images

A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Pezeshkian ya bayyana cewa Iran ba ta da al’adar kai hari da farko haka kawai.

Kasar Iran ta yi kakkausan gargaɗi

A cikin sakon, Shugaba Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa Iran ba ta kai hari da farko ba ya nufin za ta ɗauki raini a kawo mata hari har gida ba.

Ya ce:

“Mun sha faɗa sau da yawa cewa Iran ba ta kai hare-haren da farko, amma za mu mayar da martani mai ƙarfi idan aka kai hari kan ababen more rayuwarmu ko cibiyoyin tattalin arziƙinmu.”

Wannan furuci na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya, inda ake samun zargin juna tsakanin ƙasashe kan batun tsaro da farmaki.

Iran ta gargaɗi ƙasashen Gabas ta Tsakiya

Shugaban Iran ya kuma aika da saƙo kai tsaye ga ƙasashen yankin, yana mai gargadin su kan abin da ka iya jawo rikici da rashin zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Mayakan Houthi sun shigawa Iran yaki, sun yi ruwan wuta a Isra'ila

Iran ta ce za ta mayar da martani ga duk masu kawo mata hari
Jagoran addini na Iran Mojtba Khamenei, Shugaban Amurka Donald Trump Hoto: Reza B, Andrew Caballero-Reynolds
Source: Twitter

Ya ce:

"Ga ƙasashen yankin, idan kuna son ci gaba da tsaro, kada ku bari maƙiyanmu su riƙa yakar mu daga cikin ƙasashenku.”

Pezeshkian ya nuna cewa bai wa wasu ƙasashe ko ƙungiyoyi damar amfani da ƙasashen yankin wajen kai hare-hare kan Iran na iya jefa yankin cikin rikici mai tsanani.

Gargaɗin na zama kamar wani yunƙuri na Iran na hana faɗaɗa rikici a yankin, tare da jaddada cewa za ta kare kanta daga duk wata barazana.

Za a shigarwa Isra'ila yaƙi da Iran

A baya, mun wallafa cewa rahotanni sun nuna cewa kasar Uganda ta nuna alamun shiga yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya domin taya Isra'ila kai hare-haren soji Iran.

Babban hafsun soja a kasar, Muhoozi Kainerugaba ya bayyana cewa Isra'ila ta taimaka musu a baya, lokaci ya yi da za su rama wa kura aniyarta a wannan yakin.

Hakan na zuwa ne yayin da aka shiga wata guda ana gwabza yaki da Iran bayan hare-haren da Isra'ila da Amurka suka kaddamar a Tehran da ya salwantar da rayuka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng