Pakistan Ta Gana da Iran, An Taɓo Batun Sulhu da Amurka
- Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif ya tattauna da Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian a kan rikicin yankin
- Pakistan ta sake yin Allah-wadai da hare-haren Isra’ila a Iran yayin da ta ke ƙoƙarin shiga tsakani domin a hau teburin sulhu
- Iran ta yi martani a kan yunkurin da Pakistan ke yi na ganin ta zama mahadar Amurka da Iran domin kawo karshen rikicin
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Pakistan– Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif, ya bayyana cewa ya yi wata muhimmiyar tattaunawa ta wayar tarho da shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian.
Shehbaz Sharif ya ce sun shafe sama da awa guda suna magana game da tashin hankalin da Amurka da Isra'ila suka fara a watan Fabarairu, 2026.

Source: Twitter
A cikin saƙon da ya wallafa a shafin X, Sharif ya ce tattaunawar ta mayar da hankali ne kan halin da ake ciki a yankin, musamman rikicin da ke ƙara kamari tsakanin Iran da Isra’ila.
Pakistan ta yi magana da kasar Iran
Pakistan ta gana da Iran a dai-dai lokacin da ta nuna sha'awar zama dandalin sulhun da zai kawo karshen yaƙi'n Gabas ta Tsakiya.
Sanarwar Shehbaz Sharif ta ce:
“Na yi wata cikakkiyar tattaunawa ta wayar tarho da ɗan uwana Shugaba Masoud Pezeshkian na Iran a yau, wadda ta ɗauki sama da awa guda.”
Firaministan ya bayyana cewa Pakistan na ci gaba da nuna damuwa kan halin da ake ciki, inda ya ce ƙasarsa na goyon bayan zaman lafiya da tattaunawa a yankin
Shehbaz Sharif ya kuma nuna damuwa kan hare-haren da ake kai wa Iran, yana mai cewa hakan na ƙara jefa yankin cikin tashin hankali.
Ya ce:
“Na sake jaddada Allah-wadan Pakistan kan ci gaba da hare-haren Isra’ila a Iran, daga ciki har da sababbin hare-haren da aka kai kan kayayyakin more rayuwa na fararen hula.”
Haka kuma, ya bayyana goyon bayan Pakistan ga al’ummar Iran, yana mai yaba jarumtar su a wannan lokaci mai cike da ƙalubale.
Pakistan ta damu kan harin Iran
A ci gaba da bayaninsa, Sharif ya ce ya miƙa ta’aziyyarsa ga al’ummar Iran kan asarar rayuka da aka yi sakamakon rikicin.
Ya ce:
“Na kuma miƙa ta’aziyyata kan wannan mummunan asarar rayuka, tare da yin addu’ar samun sauƙin murmurewa ga waɗanda suka jikkata da kuma waɗanda suka rasa matsugunansu.”

Source: Getty Images
Firaministan ya ƙara da cewa ya gode wa shugaban Iran kan yabon da ya yi wa ƙoƙarin Pakistan na tabbatar da zaman lafiya a yankin.
Ya ce:
“Na kuma gode masa kan yabon da ya yi wa ƙoƙarin Pakistan wajen inganta zaman lafiya da sauƙaƙa tattaunawa a yankin.”
Sharif ya bayyana cewa Pakistan na ci gaba da tattaunawa da ƙasashe daban-daban domin rage tashin hankali, daga ciki har da Amurka da ƙasashen Larabawa da na Musulmi.
A cewarsa:
“Na sanar da shi cewa Pakistan na ci gaba da hulɗar diflomasiyya da Amurka da ƙasashen Larabawa da na Musulmi domin samar da tattaunawa da rage tashin hankali.”
Houthi ta shigar wa Iran yaƙi
A baya, kun ji cewa rikicin Gabas ta Tsakiya na ƙara tsananta yayin da mayakan Houthi da ke kasar Yemen suka fara kai harin makamai kan Isra’ila.
Matakin na nuna yiwuwar faɗaɗa yaƙin da ke gudana da kuma ƙarin tashin hankali a Gabas ta Tsakiya da zai iya shafar duniya yayin da kowa ke ɗaukar ɓangare.
Tun da farko dai dama Hotuthi ta yi gargadi tare da kafa sharudan guda uku da za su iya jawowa ta shiga yakin kafin fara kai hare-haren a kan Isra'ila.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


