Rasha Tana Samun Miliyoyin Daloli a Kullum saboda Yaƙin Iran, Amurka da Isra'ila
- Yayin da duniya ke kuka da matsalolin da yakin Iran, Amurka da Rasha ke jawo wa, Rasha na kwashe gwaggwabar riba daga rikicin
- Rahotanni sun bayyanar da aƙalla, kasar Rasha na samun akalla Dala miliyan 760 a kullum sakamakon rikicin da ya rincabe a Gabas ta Tsakiya
- Ana hasashen kudin shiga da Vladimir Putin ke samar wa kasarsa zai iya kaiwa Dala biliyan 386 idan rikicin ya ɗauki lokaci bai mutu ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Ƙasar Rasha– Wani rahoto ya gani cewa Shugaban Rasha, Vladimir Putin, na samun kudin shiga mai yawa sakamakon rikicin Gabas ta Tsakiya.
Wannan karin kudi ya samu ne daga sayar da mai yayin da rikicin Iran ke ƙara jawo cikas ga safarar makamashi a fadin duniya.

Source: Facebook
Telegraph UK ta ruwaito cewa Putin na samun akalla Dala miliyan 760 a kowace rana sakamakon tashin farashin mai da kuma sauƙaƙe wasu daga cikin takunkumi da aka sanya kan ƙasar.
Rasha na samun tagomashi daga yaƙin Iran
MSN ta wallafa cewa a cewar cibiyar nazarin tattalin arziki ta Kyiv, kudin da Rasha ke samu daga mai da iskar gas zai ninka daga kusan Dala biliyan 12 zuwa kusan Dala biliyan 24 a cikin wannan wata kaɗai.
Wannan na zuwa ne yayin da kasuwar makamashi ta duniya ke fuskantar rikici sakamakon matakan da Iran ta ɗauka na dakatar da zirga-zirgar mai a mashigar Hormuz.
Ko da rikicin zai ƙare cikin makonni masu zuwa, ana hasashen cewa Rasha za ta samu kusan Dala biliyan 218.5 daga mai da iskar gas a shekarar nan.
Idan kuma rikicin ya ja har na tsawon watanni shida, kudin shiga na Rasha daga fitar da mai zai iya kaiwa Dala biliyan 386.5, wanda ya zarce hasashen farko da 188% kafin rikicin ya fara.
Bukatar Rasha ga kamfanonin mai
A wani taro da aka gudanar a Kremlin, Putin ya bukaci kamfanonin mai da gas na Rasha su yi amfani da karin kudin da suka samu wajen rage basussukansu a cikin gida.
Rikicin da ya dabaibaye kasuwar makamashi ya kara bai wa Rasha damar cin riba musamman bayan matakin da Donald Trump ya dauka na sassauta wasu takunkumi a kan ƙasar.

Source: Getty Images
Farashin danyen mai na Brent ya tashi da 38% zuwa kusan Dala 100 kan kowace ganga, yayin da farashin man Rasha ya tashi fiye da haka da 72%.
Kafin wannan lokaci, Rasha na sayar da mai ga Indiya da rangwamen Dala 9 kasa da farashin Brent, amma yanzu wannan rangwame ya gushe.
An gano Rasha na taimakon Iran
A baya, mun wallafa cewa a yayin da ake ci gaba da gwabza yakin Gabas ta Tsakiya, rahotanni sun fara zargin cewa Russia tana kai wa Iran dauki da kaya iri-iri.
Wani rahoto ya yi zargin cewa Shugaban Rasha, Vladimir Putin na shirin aikewa Iran jiragen yaki marasa matuka, magunguna da sauran kayan amfani da Za a bukata.
Shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky ya zargi Rasha da ba Iran bayanan sirri, yana mai cewa yana da hujjoji da za su tabbatar da dukkanin zarge-zargen.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


