Yaki da Iran: Sabani Ya Shiga tsakanin Trump da Netanyahu, Sun Yi Musayar Yawu
- Donald Trump ya ki amincewa da bukatar sanya hannu don 'yan Iran su fita tituna yin zanga-zanga domin karbar gwamnatin kasarsu daga IRGC
- Benjamin Netanyahu wanda ya gabatar da buakatar, ya yi ikirarin cewa gwamnatin Iran na cikin rudani, don haka yanzu ne lokacin kifar da ita
- Duk da cewa Trump ya shiga yaki da Iran saboda 'matsin lambar Isra'ila,' wannan karon, Shugaban na Amurka ya juya wa Netanyahu baya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Amurka - Shugaban Amurka Donald Trump ya yi fatali da bukatar Firayim Ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, na hada gwiwa don tsara wa al'ummar Iran yadda za su su fito su kifar da gwamnatin kasarsu.
Wannan tattaunawa ta afku ne a daren Talatar da ta gabata, biyo bayan kashe manyan jami'an tsaron Iran, Ali Larijani da Gholamreza Soleimani, da Isra'ila ta yi.

Source: Getty Images
Trump ya yi watsi da bukatar Netanyahu
Netanyahu ya bayyana wa Trump ta wayar tarho cewa gwamnatin Iran tana cikin "yanayin rudani," saboda haka wannan ne lokaci mafi dace na tunzura jama'a su fito kan tituna, in ji rahoton Times of Israel.
Sai dai, Trump ya nuna fargabar cewa yin hakan zai janyo kisan kiyashi ga farar hula a lokacin da suke kan tituna suna zanga zangar.
Trump ya bayyana wa Netanyahu cewa:
"Me ya sa za mu gaya wa mutane su fito kan tituna alhalin mun san karkashe su kawai za a yi?"
A karshen wayar dai an ce shugabannin biyu sun amince su jingine wannan batu har zuwa washegari, ranar da 'yan Iran ke gudanar da bikin gargajiya na "Persian Fire Festival," don ganin ko jama'a za su yi zanga zangar a kashin kansu.
Trump, Netanyahu sun sha kunya a Iran
Manufar ita ce idan jama'a suka fara zanga-zangar da kansu, to sai shugabannin biyu su fito su goyi bayansu. Sai dai kash, babu wata gagarumar zanga-zanga da ta afku a fadin kasar ta Iran, cewar rahoton Axios.
Jami'an Amurka da na Isra'ila sun bayyana cewa al'ummar Iran suna cikin tsananin tsoron martanin dakarun IRGC, musamman duba da yadda aka murkushe zanga-zangar farkon shekarar nan.
Ko da yake Netanyahu ya fito fili ya bukaci 'yan Iran din su yi bikin nasu yayin da Isra'ila ke luguden wuta, kalilan ne kawai suka iya fitowa kan tituna saboda fargabar daukar fansa daga gwamnatin Tehran.

Source: Getty Images
Sabanin Trump da Netanyahu kan Iran
Jakadan Isra'ila a Amurka, Yechiel Leiter, ya bayyana cewa dabararsu ita ce raunana karfin gwamnatin Iran na murkushe masu adawa, domin bai wa 'yan kasar damar "karbar ragamar rayuwarsu."
A gefe guda kuma, Trump yana ci gaba da neman hanyoyin diflomasiyya wadanda za su iya barin wasu sassa na gwamnatin Iran a raye, muddin aka cimma matsaya.
Netanyahu ya nuna rashin amincewarsa da cewa za a iya cimma wata yarjejeniyar sulhu mai gamsarwa nan kusa, in ji rahoton Times of India.
A cewar jami'an Isra'ila, kisan Gholamreza Soleimani, wanda shi ne ke da alhakin murkushe zanga-zanga, an yi shi ne domin share fage ga al'umma su yi tawaye, amma har yanzu babu alamar wannan tawayen.
Matsalar da Amurka ta shiga a yakin Iran
A wani labari, mun ruwaito cewa, kudaden ruwan karbar jinginar gida a Amurka sun tashi daga kashi biyar zuwa kashi shida sakamakon yakin da ake fafatawa da Iran.
Masanin tattalin arziki na Zillow ya yi gargadin cewa tashin farashin makamashi zai iya rage yawan sayar da gidaje a daukacin shekarar nan.
Shugaba Donald Trump ya rage tsauraran dokoki domin saukaka wa yan kasa hanyoyin mallakar gidaje ta hanyar amfani da wasu fasahohi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


