Magana Ta Fito: Trump Ya Fadi Masu Kawo Masa Cikas a Nasarar Yaki da Iran
- Shugaban Amurka, Donald Trump ya zargi wasu Amurkawa da ba su da kishin kasa da neman ganin gazawar kasar a yaki da Iran
- Trump ya ce yana zargin ‘yan adawa da kokarin rage tasirin nasarar soji a yakin Amurka da Isra’ila da Iran a Gabas ta Tsakiya
- Trump ya jaddada cewa jama’ar Amurka na fahimtar abin da ke faruwa, yana mai cewa kasar ce farko gaba da komai
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya nuna damuwa game da wasu da ya kira 'munafukai' da ke neman ganin ya gaza.
Trump yana magana ne kan yaki da ake ci gaba da yi a Gabas ta Tsakiya tsakanin Iran da Isra'ila wacce Amurka ke goya wa baya.

Source: Getty Images
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce yan adawa a Amurka masu tsattsauran ra'ayi ba su son nasararsa a yaki da Iran.
Yadda yaki ya barke tsakanin Iran da Isra'ila
Wannan korafi na Trump na zuwa ne yayin da ake ci gaba da yaki tsakanin Iran da Isra'ila a Gabas ta Tsakiya wanda ya jawo sukar kasashen duniya da dama.
A yanzu, yakin ya shafe kusan wata guda kenan ana yi wanda ya jawo asarar rayuka da duniyoyi daga kowane bangare da ke cikin yakin.
An fara kai hari ne a a ranar 28 ga watan Fabrairun shekarar 2026 wanda ya yi sanadiyar rasa ran jagoran addinin Musulunci a Iran, Ayatollah Ali Khamenei da wasu manyan jami'an tsaron kasar.

Source: Twitter
Zarge-zargen da Trump ke yi wa yan siyasa
Trump ya zargi yan siyasa da kokarin kawo cikas ga abin da ya bayyana a matsayin “babbar nasarar soji” a yakin Amurka da Isra’ila ke yi da Iran.
“’Yan Democrat masu tsattsauran ra’ayi da ke kin kasa na kokarin haddasa rikici a cikin gida domin rage darajar wannan babbar nasara da muke samu a Iran.”
Shugaba Trump ya ce mutanen kwata-kwata ba su son ganin Amurka da Amurkawa na cin nasara yayin yaki da Iran a Gabas ta Tsakiya.
Sai dai ya ce jama'ar Amurka gaba daya na fahimtar abin da ke faruwa wanda hakan ke sa su gane masu son kasar a cikin zuciyarsu.
Ya kara da cewa:
“Ba sa son ganin muna yin nasara sosai da karfi, amma jama’ar Amurka na fahimtar abin da ke faruwa. Amurka ce farko!”
Bukatu 15 da Trump ya tura ga Iran
Mun ba ku labarin cewa Shugaba Donald Trump ya sanar da cewa Amurka tana tattaunawa da Iran yanzu haka kan wani tsarin zaman lafiya, kuma har an gabatar da bukatu 15.
Daga cikin bukatun da Amurka ta gabatar, akwai tilasci ga Iran na daina tace sinadarin uranium tare da lalata dukkan kayyakin nukiliyarta.
Amurka na duba yiwuwar tsagaita bude wuta na tsawon wata guda domin ba da damar tattaunawa kan wannan sabon tsarin sulhun.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

