Martanin Iran kan Bukatar Trump na Sulhu da Trump, Ta Fadi yadda Yakin Zai Kare

Martanin Iran kan Bukatar Trump na Sulhu da Trump, Ta Fadi yadda Yakin Zai Kare

  • Kasar Iran ta yi martani mai zafi ga Amurka bayan bukatar Donald Trump na da shirin zaman lafiya a yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya
  • Iran ta bakin wani jami'i ta ce ita ce za ta yanke lokacin ƙarshen yaƙin inda ta ce ba zai ƙare ba sai lokacin da ta ga dama
  • Tehran ta gabatar da sharudda biyar ciki har da diyya, dakatar da hare-hare da tabbatar da ikon ta kan mashigar Hormuz

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tehran, Iran - Kasar Iran ta yi martani bayan samun bukatar shugaban Amurka, Donald Trump na shirin zaman lafiya a yakin da ake yi.

Kasar ta yi watsi da shirin zaman lafiya da Amurka ta gabatar domin kawo ƙarshen yaƙin Gabas ta Tsakiya, kamar yadda gidan talabijin na ƙasar ya ruwaito.

Kara karanta wannan

Yaƙi da Iran ya raba kan Amurkawa, ana ganin Trump ya fara wuce gona da iri

Iran ta yi wasti da bukatar Amurka a yakinta da Isra'ila
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu da sabon jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei. Hoto: Gil Cohen-Magen.
Source: Getty Images

Iran ta yi watsi da bukatar Amurka

Wani babban jami’i a Iran da ba a bayyana sunansa ba ya ce kasar ta yi watsi da wannan bukata da cewa babu ita a ciki, cewar rahoton BBC.

An ji yo jami'in yana mai cewa:

“Iran ta ƙi shirin Amurka na kawo ƙarshen yaƙin da ake ciki.”

Ya ƙara da cewa karshen yaƙin zai zo ne kawai lokacin da Iran ta yanke shawara, ba lokacin da Donald Trump ke hasashen zai ƙare ba.

Har yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnatin Iran kan wannan shiri, yayin da ministan harkokin wajen ƙasar, Abbas Araghchi, bai yi magana a kai ba.

Sai dai kafafen yaɗa labarai na Iran kamar Mehr da Tasnim sun ruwaito wanda ya fara bayyana wannan batu.

Iran ta fadi lokacin da za ta kawo karshen yaki da Isra'ila
Jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei da Shugaba Donald Trump. Hoto: Iran Military Media, Donald J Trump.
Source: Facebook

Sharudan da Iran ta gabatar ga Amurka

A baya, wasu manyan jami’an Pakistan sun ce sun miƙa wa Iran wani tsari mai matakai 15 da ya ƙunshi shawarwarin Amurka domin kawo ƙarshen yaƙin da ya kusan kai wata guda.

Kara karanta wannan

Iran ta ba Trump mamaki, ya fadi abin da ta yi na bazata da ya aminta da ita

Sai dai Iran ta gabatar da nata sharudda guda biyar domin kawo ƙarshen rikicin, ciki har da dakatar da hare-hare da kashe-kashe a kan ƙasar da shugabanninta, da kuma samar da tabbacin cewa ba za a sake kai hari ba.

Haka kuma, Iran na neman a biya diyya kan barnar da aka yi domin sake gina abubuwan da suka lalace sakamakon yaƙin, cewar NBC News.

Bugu da ƙari, sharuddan sun haɗa da dakatar da rikici a dukkan yankuna da kuma kan wasu ƙungiyoyi ciki har da Hezbollah.

A ƙarshe, Iran na neman a amince da haƙƙinta na mallakar iko a kan mashigar Hormuz, wadda ke da muhimmanci ga kasuwancin duniya a wannan lokaci.

Iran ta musanta shirin tattauna wa da Trump

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi ikirarin cewa ya fara tattaunawa da Iran domin duba yiwuwar kawo karshen yakin da ake yi.

Ma'aikatar harkokin wajen Iran ta fito ta yi watsi da ikirarin na Shugaban kasar Amurka kan batun fara tattaunawa da kasar.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen ya bayyana abin da Iran za ta yi maimakon tattaunawa da Amurka da Isra'ila a yakin da ake yi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.