Pakistan za Ta Shiga tsakani a Yakin da Amurka da Isra'ila ke Gwabzawa da Iran

Pakistan za Ta Shiga tsakani a Yakin da Amurka da Isra'ila ke Gwabzawa da Iran

  • Kasar Pakistan ta bayyana shirinta na zama mai shiga tsakani tsakanin Amurka da Iran a yakin da ake gwabzawa
  • Rahotanni sun ce ana shirin gudanar da tattaunawa a Islamabad domin a duba yiwuwar kawo karshen barin wuta da ake yi
  • Rikicin na ƙara dagula tattalin arzikin duniya da makamashi tun bayan da Amurka da Isra'ila suka tsire shi a Fabarairu, 2026

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Pakistan – Gwamnatin Pakistan ta bayyana cewa a shirye take ta karɓi bakuncin tattaunawa tsakanin Amurka da Iran.

Wannan na zuwa ne yayin da rahotanni daga kafafen yaɗa labarai na duniya ke nuna yiwuwar a gudanar da zaman sulhu a birnin Islamabad.

Ana son sulhu tsakanin Amurka da Iran
Shugaban Amurka, Donald Trump da jagoran addini na kasar Iran, Mojtaba Khamenei Hoto: Reza B, Andrew Caballero-Reynolds
Source: Twitter

Al-Jazeera ta wallafa cewa ya ƙara da cewa Pakistan ta dade tana goyon bayan amfani da diflomasiyya domin kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

Kara karanta wannan

Trump zai sauya salon yaki da Iran, sojojin Amurka 2,500 sun nufi Gabas ta Tsakiya

Ana son sulhu tsakanin Amurka da Iran

Arab News ta wallafa cewa Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Pakistan, Tahir Andrabi, ya ce idan ɓangarorin biyu suka amince, ƙasar za ta iya zama mai shiga tsakani domin tattaunawar.

Rahotanni sun bayyana cewa wata tawagar Amurka na iya zuwa Islamabad domin tattaunawa da jami’an Iran kan yadda za a kawo ƙarshen rikicin da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya.

Trump ya sha cewa ana sulhu da Iran batun da ta Iran din ta karyata
Shugaban Amurka Donald J Trump Hoto: Donald J Trump
Source: Getty Images

Sai dai har zuwa lokacin rubuta wannan rahoto, babu wata cikakkiyar sanarwa daga Fadar White House ko jakadancin Amurka da ke Pakistan da ta tabbatar da wannan batu.

Wasu majiyoyin diflomasiyya sun bayyana cewa an gabatar da Pakistan a matsayin ƙasa mai zaman kanta da za ta iya karɓar irin wannan muhimmin zama tsakanin Amurka da Iran.

Tasirin rikicin Iran ga duniya

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa ana samun ci gaba a tattaunawar da ake yi da Tehran, har ma ya jinkirta wasu hare-haren da aka shirya kai wa tashoshin wutar lantarki na Iran.

Kara karanta wannan

Yaki ya yi zafi, Amurka ta fara neman $200bn don ci gaba da farmakin Iran

Sai dai jami’an Iran sun musanta wannan ikirari, inda suka ce babu wata tattaunawa da ke gudana, suna mai bayyana irin waɗannan rahotanni a matsayin wani yunkuri na yaƙin tunani.

Rahotanni sun kuma nuna cewa shugaban rundunar sojin Pakistan, Syed Asim Munir, ya yi magana da Trump ta waya, kafin firaministan Pakistan Shehbaz Sharif ya tattauna da shugaban Iran Masoud Pezeshkian.

A yayin tattaunawar, Sharif ya jaddada bukatar gaggauta amfani da hanyoyin diflomasiyya domin warware rikicin, musamman ganin yadda yake barazana ga tsaron makamashi da ruwa a yankin.

Rikicin ya fara ne a ranar 28 ga Fabrairu, 2026 bayan Amurka da Isra’ila sun kai hare-hare kan cibiyoyin nukiliya da manyan shugabannin Iran.

Tun daga lokacin, an samu asarar rayuka masu yawa tare da dubunnan mutane da suka rasa muhallansu.

Iran ta kara wa Isra'ila ruwan bama-bamai

A baya mun wallafa cewa rundunar dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC), na ci gaba da kai hare-hare kan Isra'ila da sansanonin sojojin Amurka.

IRGC ta sanar da cewa ta kai hare-hare kan wurare masu muhimmanci a Isra'ila yayin da ake ci gaba da gwabza fada a yankin Gabas ta Tsakiya da Amurka da Isra'ila suka jawo.

Rundunar IRGC ta bayyana cewa ta yi amfani da makamai masu linzami da jirage marasa matuka wajen kai hare-haren, wanda a yanzu haka ke kara kazanta a yankin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng