An Yi Ruwan Makamai a Tel Aviv, Isra'ila Ta Fadi Barnar da Harin Iran Ya Yi Mata
- Wani makami mai linzami da kasar Iran ta harba ya lalata wani babban gini a birnin Tel Aviv, inda ya jikkata mutane hudu a yau Talata
- Sojojin Isra'ila sun fitar da gargadin hare-haren makaman linzami akai-akai daga Iran da Lebanon yayin da ake ci gaba da fafatawa
- Rahotanni sun bayyana cewa jami'an kwance bama bamai na ci gaba da aikin kwashe bama baman da basu kai ga tashi ba a Tel Aviv
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Isra'ila - Magajin garin Tel Aviv, Ron Huldai, ya tabbatar da cewa wani makami mai linzami da Iran ta harba ya sami wasu gine-gine a ranar Talata.
Harin, wanda ya afku a wani babban yanki dake Arewacin birnin, kuma ya ruguza bangon wani tsohon gini mai hawa uku tare da jawo watsuwar baraguzai a kan titi.

Kara karanta wannan
Yayin da Amurka ke ikirarin tattaunawa, Iran ta yi wa Isra'ila illa da makamai masu linzami

Source: Getty Images
Makaman Iran sun sauka a sassan Isra'ila
Wannan na zuwa ne yayin da fargabar hare-haren Iran ke ƙara ruruwa a birnin Tel Avi, kamar yadda rahoton Gulf News ya nuna.
Sojojin Isra'ila sun fitar da gargaɗi har sau bakwai a ranar Talata game da makaman da ake harbowa daga Iran zuwa tsakiya da kudancin ƙasar.
Haka kuma, an fitar da wasu gargaɗin guda shida kan makaman da ake harbawa daga ƙasar Lebanon a yankin Arewacin babban birnin Isra'ilan.
Kodayake sojojin Isra'ila sun ce suna kakkabe kashi 90 cikin ɗari na makaman, sun yi gargaɗin cewa garkuwarsu ba ta da tabbacin kare harin makaman da kashi 100.
Barnar da harin Iran ya yi wa Isra'ila
Kafofin yaɗa labaran Isra'ila, ciki har da gidan rediyon sojojin kasar, sun bayyana cewa ‘yan sanda sun sanar da cewa makamin da ya afka wa ginin mai hawa uku yana ɗauke da kawuna huɗu, inda kowanne ke ɗauke da kusan kilogiram 100 na bama-bamai.
Hukumar agajin gaggawa ta Magen David Adom (MDA) ta fitar da bidiyon da ke nuna irin gagarumar barnar da fashewar ta yi a cikin gidajen mutane, a cewar rahoton Arab Times.

Source: Getty Images
Ana aikin kwashe bama-bamai a Tel Aviv
Hukumar ta MDA ta bayyana cewa ta duba tare da sallamar mutane huɗu waɗanda suka sami raunuka da ba su yi tsanani ba daga harin.
Da farko an bayar da rahoton mutane shida ne suka jikkata, amma daga baya aka rage yawan zuwa huɗu. Majiyoyi sun nuna cewa mutanen sun shaƙi hayaƙi ne sakamakon wata ƙaramar gobara da fashewar ta haifar.
Jami'an kiyaye bama-bamai na ‘yan sanda sun mamaye wurare daban-daban a cikin gundumar Tel Aviv domin bincike da kuma kwashe duk wani sauran makami da zai iya sake tashi.
Magajin garin ya jaddada muhimmancin bin umarnin jami'an tsaro da kuma neman mafaka a duk lokacin da aka ji ƙarar gargaɗi.
Halin da ake ciki a Isra'ila
A wani labari, mun ruwaito cewa, Isra’ila ta ayyana dokar ta-baci bayan Iran ta harba makamai masu linzami wanda ya jawo hana yawan taruwar mutane.

Kara karanta wannan
Makamin da Iran ta harba ya keta tsaron Isra'ila, ya fada kusa da cibiyar nukiliya
An kwashe marasa lafiya zuwa karkashin kasa a asibitoci yayin da aka kira sojojin ajiyar gaggawa domin kare iyakoki daga hare-haren makamai.
Duk da barazanar, wasu mazauna Tel Aviv sun nuna kwarin gwiwa da tsarin kariya na sararin samaniya, suna goyon bayan matakin soja na Isra'ila.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
