Kasashe 7 da Suka Ki Amincewa da Bukatar Trump na Tura Jiragen Yaki zuwa Hormuz

Kasashe 7 da Suka Ki Amincewa da Bukatar Trump na Tura Jiragen Yaki zuwa Hormuz

Shugabannin ƙasashen da ke cikin ƙungiyar NATO sun yi watsi da kiran shugaban Amurka Donald Trump na neman su sa hannu a yaƙin da yake fafatawa da Iran, duk da matsin lamba mai ƙarfi daga Washington.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Bayan ƙasashen Japan, da Burtaniya sun bayyana cewa ba su da shirin tura jiragen yaƙi zuwa mashigar ruwan Hormuz, an samu ƙarin ƙasashe biyar da suma suka ƙi amincewa da buƙatar Trump.

Wasu kasashe 7 sun ki amincewa da bukatar Trump na tura jiragen yaki zuwa Hormuz
Shugabannin kasashen NATO suna gudanar da taron kungiyar karo na 76 a Netherlands. Hoto: Beata Zawrzel/NurPhoto via Getty Images
Source: Getty Images

Yaki da Iran: Trump ya sha suka daga NATO

Shugaba Trump dai ya bayyana cewa gwamnatinsa ta tuntuɓi ƙasashe bakwai inda take sa ran za su taimaka wajen samar da tsaro a mashigar ruwan da Iran ta toshe, in ji rahoton The Independent.

Trump ya shaida wa manema labarai cewa:

Kara karanta wannan

Donald Trump ya faɗi lokacin da Iran za ta hau teburin tattaunawa

"Ina buƙatar waɗannan ƙasashe su shigo su kare yankunansu, domin hanyarsu ce su ma. Ta hanyar ne dai suke samun makamashin su."

Sai dai, daga alama, Trump ba zai samu goyon bayan ƙasashen da yake neman taimakonsu ba, sai dai kuma ya sauya wani salon na kare mashigar daga hare-haren Iran.

"Wannan ba yaƙin NATO ba ne," in ji wani mai magana da yawun shugaban Jamus, Friedrich Merz.

Ya kara da cewa:

"NATO ƙungiyar ƙawance ce ta kare yankunan mambobinta. Amurka ba ta nemi shawararmu ba kafin fara wannan yaƙin, saboda haka mun yi amanna wannan ba hurumin NATO ba ne ko na gwamnatin Jamus."

Kasashe 7 da suka yi watsi da bukatar Trump

Ga bayani dalla dalla kan yadda ƙasashen suka bayyana matsayarsu:

1. Jamus

Ministan Tsaron Jamus, Boris Pistorius, ya yi watsi da bukatar Amurka inda ya jefa wa Trump tambaya game da tasirin rundunar sojin ruwan Amurka a kare mashigar Hormuz.

"Wannan ba yaƙinmu ba ne. Ba mu ne muka fara shi ba. Me Donald Trump yake sa ran wasu ƙalilan daga cikin jiragen yaƙin Turai za su iya yi a Hormuz wanda rundunar sojin ruwan Amurka mai ƙarfi ba za ta iya yi ba?" in ji Pistorius.

Kara karanta wannan

Trump ya fallasa dabarar da Iran take amfani da ita a yaki da Isra'ila

Jamus ta yi hakan ne duk da gargaɗin Trump na cewa rashin taimaka wa Washington zai iya shafar makomar ƙawancen na NATO, cewar rahoton Reuters.

2. Japan

Firayim Ministar Japan, Sanae Takaichi ta ce tura jiragen yaki zuwa Hormuz abu ne mai wahala.
Firayim Ministar Japan, Sanae Takaichi. Hoto: @takaichi_sanae
Source: Twitter

Firayim Ministar Japan, Sanae Takaichi ta bayyana cewa a hukumance Amurka ba ta gabatar da buƙatar neman taimako ba tukuna.

Ta bayyana cewa ta fuskar doka, tura dakarun kasar zuwa ƙasashen waje abu ne mai matuƙar wahala da sarkakiya a siyasance.

Sanae Takaichi ta shaidawa majalisar kasar cewa:

"Ba mu kai ga yanke wata shawara ba game da tura jiragen rakiya. Muna ci gaba da nazarin abin da Japan za ta iya yi ita kaɗai da kuma abin da za a iya yi a cikin tsarin doka."

Ko da yake Japan ta fara amfani da danyen man da take ajiye da shi domin daidaita kasuwa, ta ce tana ci gaba da tattaunawa da Iran domin kwantar da tarzomar.

3. Australia

Ministar sufurin Australia, Catherine King ta bayyana karara cewa ba za su tura jirgin yaƙi zuwa mashigar ruwan Hormuz ba, kamar yadda rahoton ABC News ya nuna.

Kara karanta wannan

Ana tsakiyar musayar wuta, Trump ya yi magana kan kawo karshen yaki da Iran

Ta bayyana cewa:

"Ba za mu tura jirgin ruwa zuwa mashigar ruwan Hormuz ba.
"Mun san muhimmancin hakan sosai, amma wannan ba wani abu ba ne da aka nemi taimakonmu a kansa, ko kuma muke da ra'ayin ba da gudunmawa a kai ba ne."

Catherine ta ce gudunmawar da suke bayarwa a halin yanzu ita ce tura jiragen sama zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa domin kare 'yan ƙasar Australia dake yankin.

Inabi James Paterson, wani jami'in adawa na tsaro, ya ƙara da cewa Australia ba ta da jiragen ruwan yaƙi da za su iya kare kansu daga harin jirage marasa matuƙa da makaman linzami a halin yanzu.

4. Birtaniya

Firayim Ministan Birtaniya, Keir Starmer ya ce kasarsa ba za ta shiga wannan yaki da Amurka ke yi da Iran ba.
Firayim Ministan Birtaniya, Keir Starmer. Hoto: @Keir_Starmer
Source: Twitter

Firayim Minista Keir Starmer ya bayyana cewa Birtaniya ba za ta bari a ja ta cikin babban yaƙi ba.

Ko da yake ƙasar tana tunanin tura na'urorin kakkabo makamai daga sararin sama, jami'ai sun yi gargaɗin cewa tura manyan jiragen yaƙi zai iya ƙara rura wutar rikicin.

Kara karanta wannan

An yi yunkurin sasanta Amurka da Iran, sakamakon bai yiwa kasashe 2 dadi ba

Starmer ya ce gwamnatinsa ta kuduri aniyar tsayawa tsayin daka domin kare muradun Birtaniya komai matsin lambar da ake yi masa.

5. Italiya

Ministan wajen Italiya, Antonio Tajani, ya bayyana cewa diflomaasiyya ita ce hanyar da ta dace wajen magance rikicin mashigar Hormuz.

Ya ce Italiya tana da runduna a Read Sea domin ba ta kariya, amma ba shi da masaniyar ko za a tura dakaru zuwa mashigar ruwan Hormuz a halin yanzu.

6. Faransa

Gwamnatin Faransa ta fitar da sanarwar cewa ba ta da shirin tura dakarun soja ruwa mashigar ruwan Hormuz, kamar yadda France 24 ta ruwaito.

Ministar tsaro Catherine Vautrin ta jaddada cewa Faransa ba ta cikin yaƙin da ake yi a Gabas Ta Tsakiya, kuma tana son ganin an samu zaman lafiya ne maimakon ƙara ta'azzara rikici.

Ta kuma bayyana cewa har yanzu burin da Amurka da Isra'ila suke son cimma a wannan yaƙin ba a fayyace yake ba, balle a ce wani ya dauki matsaya.

Kara karanta wannan

Ministan tsaro ya faɗi dalilin da ya sa ƴan ta'adda suka fi kai hare hare a Ramadan

7. Girka

Gwamnatin Girka ta e ba za ta tura jiragen yaki zuwa mashigar ruwan Hormuz ba.
Kyriakos Mitsotakis, Firayin Ministan kasar Girka yana jawabi a zauren majalisa. Hoto: @pavlmarin
Source: Twitter

Girka ba za ta shiga kowane aikin soja a mashigin Hormuz ba, in ji kakakin gwamnatin Girka Pavlos Marinakis a ranar Litinin.

Girka za ta shiga ne kawai a cikin aikin sojin ruwa na Tarayyar Turai mai suna "Aspides" wanda ke da alhakin kare jiragen ruwa a tekun Red Sea, in ji Marinakis a wani taron manema labarai.

Ministan wajen ƙasar George Gerapetritis, wanda yake magana a Brussels a gefen taron Majalisar Harkokin Waje ta Tarayyar Turai, ya goyi bayan wannan matsayi.

George Gerapetritis, ya ƙara da cewa Girka ba ta da nufin shiga wannan yaƙi, kodayake tana goyon bayan zirga-zirgar jiragen ruwa cikin aminci a wannan babbar mashiga, kuma tana kiran Iran da ta girmama dokokin teku na duniya.

Kasar da ke da makullin kasuwar man duniya

A wani labari, mun ruwaito cewa, kamfanin Saudi Aramco ya tabbatar da tashar da zai fitar da mai a watan Afrilu sakamakon ikon da Iran ke da shi kan mashigar Hormuz.

Kara karanta wannan

Marigayi Buhari, Pantami da manyan da aka yada labarin karyar za su yi aure

Masana sun bayyana cewa ikon Iran na amfani da jirage marasa matuka zai sa yaƙinta da Amurka, Iran ya yi tsayi fiye da yadda Trump ke tsammani.

Ana fargabar 'yan Houthi za su iya kai hari tashar Yanbu dake Saudiyya, wanda hakan zai katse hanyar karshe ta fitar da man fetur daga kasar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com