Rudani: Shugaban Majalisar Tsaron Iran Ya Fitar da Sanarwa bayan Isra'ila Ta Ce Ta Kashe Shi

Rudani: Shugaban Majalisar Tsaron Iran Ya Fitar da Sanarwa bayan Isra'ila Ta Ce Ta Kashe Shi

  • An shiga rudani kan batun kashe shugaban Majalisar tsaron kasar Musulunci ta Iran, Ali Larijani a yakin da ake yi da Amurka da Isra'ila
  • Ministan tsaron Isra'ila, Israel Katz ya yi ikirarin cewa sun kashe Larijani a hare-haren da suka kai Iran a daren jiya Litinin
  • Sai dai jim kadan bayan haka, jagora a tsaron Iran ya fitar da sakon jimami tare da addu'a ga sojojin kasar da aka shirya jana'izarsu yau Talata

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Israel - Gwamnatin Isra'ila ta yi ikirarin cewa hare-haren da ta kai kasar Iran a daren jiya Litinin sun yi sanadiyyar ajalin babban jami'in tsaron Jamhuriyar ta Musuluni, Ali Larijani.

Ministan tsaron Isra'ila, Israel Katz, ne ya bayyana hakan, inda ya bayyana cewa an kashe Ali Larijani, a wani hari da aka kai yayin yaƙin da ke gudana tsakanin Iran, Amurka da Isra’ila.

Kara karanta wannan

Yaki ya yi zafi, Isra'ila ta kashe babban kwamanda a Iran

Ali Larijani.
Shugaban Majalisar tsaron Iran, Sli Larijani Hoto: @alilarijani_ir
Source: Twitter

Rahoton tashar Al-Jazeera ya nuna cewa har zuwa yanzu Iran ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba domin tabbatar ko karyata wannan rahoto.

Rahotanni sun ce Larijani yana cikin manyan jagororin da ke tsara dabarun tsaron Iran a lokacin wannan yaƙi.

Ali Larijani ya fitar da sako a shafinsa

Sai dai jim kadan bayan ikirarin Isra'ila, Ali Larjani ya wallafa sakon jimamin rasuwar sojojin ruwan Iran a shafinsa na X da safiyar yau Talata, wadanda ya ayyana matsayin shahidai.

Wannan sako ya haifar da shakku kan ikirarin Ministan Isra'ila, wanda ya ce sun kashe Larijani tun a daren ranar Litinin.

Yayin da Iran ta shirya jana'izar sojojin ruwam da Amurka da Isra'ila suka kashe yau Talara, Larijani ya wallafa sako cewa:

"A daidai lokacin jana'izar jaruman sojojin ruwan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, al'ummar wannan kasa za su ci gaba da tunawa da su a zukatansu.

Kara karanta wannan

Shugaba Trump ya samu bayani, an kashe shugabannin kasar Musulunci ta Iran

"Kuma wadannan shahidai za su karfafa rundunar sojojin Jamhuriyar Musulunci na tsawon shekaru masu zuwa. Ina rokon Allah Madaukakin Sarki da ya ba wadannan shahidai mafi girman matsayi."
Firaministan Isra'ila.
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu yana jawabi a wani taron kasa da kasa Hoto: Gil Cohen Magen
Source: Getty Images

Gwamnatin Iran ba ta ce komai ba

Ali Larijani ya kasance ɗaya daga cikin fitattun ‘yan siyasar Iran da aka sani da salon shugabanci mai natsuwa a cikin tsarin gwamnatin ƙasar.

A watan Agustan 2025 ne aka sake naɗa shi a matsayin shugaban majalisar tsaron ƙasar, inda ya zama ɗaya daga cikin manyan masu yanke shawara a gwamnatin Iran musamman bayan fara yaƙi da Amurka da Isra’ila suka.

Har yanzu dai ana jiran martanin hukumomin Iran kan rahoton da Isra’ila ta fitar game da mutuwarsa.

Trump ya yi ikirarin kashe manyan Iran

A wani rahoton, kun ji cewa Shugaba Donald Trump ya yi ikirarin cewa hare-haren Amurka da Isra'ila sun yi ajalin manyan jagorori na Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

A cewar Trump, hare-haren da aka kai kan wasu tarukan shugabannin Iran sun yi sanadin hallaka su a yakin da ake ci gaba da yi a Gabas ta Tsakiya.

Furucin na Shugaba Trump na zuwa ne a daidai lokacin da yaƙin da Amurka da Isra’ila ke yi da Iran ke ci gaba da tsananta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262