Wata Sabuwa: Iran Ta Aika Sako Mai Zafi ga Kasashen Musulmi kan Yakinta da Amurka, Isra'ila
- Yaki na ci gaba da gudana tsakanin kasashen Amurka, Isra'ila da Jamhuriyar Musulunci ta Iran a yankin Gabas ta Tsakiya
- Wani babban jami'i a gwamnatin Iran, Ali Larijani, ya aika da sako ga kasashen Musulmi kan yakin da ake yi
- Ali Larijani ya koka kan yadda Amurka da Isra'ila suka kaddamar da hare-hare kan Iran yayin da ake tsaka da tattaunawa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tehran - Babban jami’i a gwamnatin Iran, Ali Larijani, ya fitar da wani saƙo zuwa ga Musulmin duniya baki ɗaya da kuma gwamnatocin ƙasashen Musulmi.
Ali Larijani ya yi kiran hadin kai tare da sukar abin da ya bayyana a matsayin cin zarafi daga Amurka da Isra’ila a kan Iran.

Source: Twitter
Hakan na kunshe ne a cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin, 16 ga watan Maris 2026.
Larijani ya tabo hare-haren Amurka a Iran
A cikin sanarwar, Larijani ya ce an kai wa Iran abin da ya kira harin yaudara na Amurka da Isra'ila wanda aka gudanar a lokacin da ake tsaka da tattaunawa.
Ya ce harin ya yi sanadin mutuwar wani babban kwamandan juyin juya halin Musulunci gami da fararen hula da shugabannin sojoji da dama.
A cewar Larijani, al'ummar Iran sun mayar da martani da ‘juriya ta ƙasa da ta Musulunci’, wadda ya ce ta hana maharan cimma burinsu.
Me ya ce kan kasashen Musulmi?
Jami’in na Iran ya kuma soki abin da ya bayyana a matsayin rashin nuna goyon baya daga yawancin ƙasashen Musulmi yayin wannan fafatawa.
Yayin da yake amincewa da cewa wasu gwamnatocin sun nuna goyon bayan siyasa mai iyaka, ya ce galibin duniyar Musulmi sun yi shiru.
Larijani ya kafa hujjar cewa juriyar Iran a kan Amurka, wadda aka kira a cikin sanarwar da ‘Babban Shaiɗan’, da Isra’ila, wato ‘Ƙaramin Shaiɗan’, tana da tushe ne a kan kare muradun duniyar Musulmi.

Kara karanta wannan
To fa: Musayar wutar da ake tsakanin Amurka, Isra'ila da Iran ta shiga wani muhimmin mataki
Ya yi tambaya kan ko matsayin wasu gwamnatocin Musulmi ya yi daidai da koyarwar Musulunci, inda ya ambaci hadisin Annabi (SAW) da ke ƙarfafa Musulmi su amsa kiran neman taimako daga ‘yan uwansu Musulmai.
Meyasa Iran ke kai hari a wasu kasashe?
Saƙon ya kuma tabo sukar da wasu ƙasashe suka yi wa Iran na kai hari kan sansanonin sojin Amurka da kadarorinsu da ke cikin ƙasashensu.
Larijani ya kafa hujjar cewa Iran ba za ta iya yin shiru ba idan ana amfani da waɗancan sansanonin wajen kai mata hari.
“Fafatawar yau, a zahiri, tsakanin Amurka da Isra’ila ne a gefe ɗaya, da kuma Musulman Iran da dakarun juriya a ɗayan gefen. A wane bangarr kuke kenan?”
- Ali Larijani

Source: Twitter
Larijani ya bayyana rashin jin daɗinsa kan abin da ya kira rashin goyon baya daga ƙasashen da Musulmi suka fi yawa lokacin da aka kai wa Iran hari.
“Wasu ƙasashe ma sun wuce gona da iri, inda suka ayyana Iran a matsayin abokiyar gabarsu kawai don ta nufi sansanonin Amurka, gami da kadarorin Amurka da Isra’ila da ke cikin yankunansu."
- Ali Larijani
Daga ƙarshe, Larijani ya yi kiran haɗin kan Musulmi, inda ya jaddada cewa Iran ba ta neman “mamaye” yankin.

Kara karanta wannan
Iran ta fadi sharadin tsagaita wuta kan Amurka, Isra'ila bayan kuskuren farmakinta
“Kun sani sarai cewa Amurka ba ta da amana, kuma Isra’ila, a zahiri, makiya ce a gare ku.”
- Ali Larijani
Makaman Iran sun yi barna a Isra'ila
A wani labarin kuma, kun ji cewa Jamhuriyar Musulunci Iran ta harba makamai masu linzami kan wasu wurare a kasar Isra'ila.
faɗawar makamai a wurare da dama a tsakiyar Isra'ila ranar Litinin biyo bayan luguden makamai masu linzami da Iran ta harba.
Hukumar kashe gobara da ceto ta Isra'ila ta bayyana cewa wurare 10 ne a faɗin ƙasar suka samu lalacewa sakamakon baraguzan makaman da aka kakkabo.
Asali: Legit.ng
