Donald Trump Ya Faɗi Lokacin da Iran za Ta Hau Teburin Tattaunawa

Donald Trump Ya Faɗi Lokacin da Iran za Ta Hau Teburin Tattaunawa

  • Shugaba Donald Trump ya ce kasar Iran ta matsu domin a fara tattaunawa da Amurka game da yakin da ake yi
  • Trump ya bayyana cewa har yanzu bai ga alamun cewa Iran ta shirya yin abin da ake bukata domin sulhu ba
  • Shugaban Amurka ya kuma ce yana tattaunawa da wasu ƙasashe kan yadda za a kula da mashigar ruwa ta Hormuz

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

United States – Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa Iran na nuna matuƙar sha’awar fara tattaunawa da Amurka duk da rikicin da ke tsakaninsu a halin yanzu.

Trump ya faɗi haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai a cikin jirgin shugaban ƙasa na Amurka, wato Air Force One, a lokacin wata tafiya.

Kara karanta wannan

Ana tsakiyar musayar wuta, Trump ya yi magana kan kawo karshen yaki da Iran

Trump ya ce Iran na neman a yi sulhu
Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian da Shugaba Donald Trump na Amurka Hoto: @drpezeshkian, @RealDonaldTrump
Source: Twitter

Al-Jazeera ta ruwaito cewa a cewarsa, Iran na son shiga tattaunawa da Amurka sosai, amma yana ganin har yanzu akwai sauran rina a kaba.

Iran na son a fara tattaunawa - Trump

Jerusalem Post ta wallafa cewa Trump na ganin Iran ba ta shirya ɗaukar matakan da ake buƙata domin warware matsalar gaba ɗaya ba.

Trump ya ce:

“Ina ganin Iran na son yin tattaunawa sosai, amma ba na zaton sun shirya yin abin da ya kamata su yi tukuna.”

Duk da haka, shugaban Amurka ya nuna cewa yana sa ran Iran za ta shiga tattaunawa da Amurka a wani lokaci nan gaba.

Ya kara da cewa:

“Ina ganin za su tattauna da mu a wani lokaci. A halin yanzu muna tafiyar da al’amura yadda ya kamata dangane da dukkanin halin da ake ciki game da Iran.”

Trump ya yi magana game da Hormuz

Kara karanta wannan

An yi yunkurin sasanta Amurka da Iran, sakamakon bai yiwa kasashe 2 dadi ba

Maganganun Trump na zuwa ne a lokacin da ake ci gaba da samun tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya, musamman dangane da barazanar ramuwar gayya daga Iran kan wasu hare-hare da ake kai mata.

A wani bangare na jawabin nasa, Trump ya bayyana cewa Amurka na tattaunawa da wasu ƙasashe domin ganin an samar da tsarin tsaro a mashigar ruwa ta Hormuz.

Wannan mashiga na daga cikin hanyoyin ruwa mafi muhimmanci a duniya wajen jigilar danyen mai da sauran kayayyaki daga yankin Gabas ta Tsakiya zuwa sauran sassan duniya.

Trump ya ce a nan gaba kadan Iran za ta tattauna da Amurka
Shugaban kasar Amurka Donald J Trump Hoto: Donald J Trump
Source: Getty Images

Trump ya ce Amurka na magana da sauran ƙasashe domin su taimaka wajen sa ido da kula da zirga-zirgar jiragen ruwa a yankin, musamman ganin yadda ake ci gaba da samun barazanar kai hare-hare daga Iran.

Sai dai a nata bangaren, Iran ta ce mashigar Hormuz a bude take ga yawancin jiragen ruwa na duniya masu jigila a hanyar.

Duk da haka, jami’an Iran sun jaddada cewa mashigar ba za ta kasance a bude ga jiragen ruwa na Amurka da na Isra’ila da kuma ƙawayensu ba.

Trump: 'Yaƙi da Iran zai kare"

A baya, mun wallafa cewa Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi magana kan lokacin da yakin da ake tsakanin Iran da Isra'ila zai zo ƙarshe yayin da aka shiga mako na uku.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Trump ya yi fatali da bukatar Putin kan yakin Amurka da Iran

Shugaba Trump ya bayyana haka ne a wata hira da manema labarai yana mai cewa zai gane lokacin da yakin ya kare idan ya ji a cikin ransa cewa lokaci ya yi a tsaya haka.

Shugaban kasar Amurka ya ce dakarun kasarsa na samun gagarumar nasara a yakin da suke yi tare da Isra'ila kan Iran run bayan da suka tsokano tashin hankali a ƙarshen Fabrairu, 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng