Rasha: Amurka Ta Fara Bakin Jini a Turai saboda Yakin Iran
- Shugabannin Turai sun soki matakin da Donald Trump ya dauka na sassauta wasu takunkumin da aka kakaba wa Rasha
- Amurka ta ba kasashe damar kwanaki 30 su sayi man Rasha domin rage matsin da kasuwar mai ke fuskanta saboda yaki da Iran
- Volodymyr Zelenskyy ya ce matakin na iya ba Moscow damar samun karin kudaden shiga yayin da yake ci gaba da yakin da Ukraine
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
USA – Shugabannin kasashen Turai sun bayyana rashin jin dadinsu kan matakin da gwamnatin Amurka ta dauka na sassauta wasu takunkumin tattalin arziki da aka kakaba wa Rasha.
A cewarsu, wannan mataki na iya kara karfafa wa Moscow gwiwa a yakin da take yi a Ukraine bayan ta fara nasarar cinikin mai a yankin.

Source: Getty Images
BBC Hausa ta wallafa cewa Fadar White House ta bayyana cewa Amurka za ta ba wasu kasashe damar sayen man Rasha na tsawon kwanaki 30 duk da takunkumin da kasashen Yamma suka kakaba mata.
kasashen Turai sun yi tir da matakin Amurka
The Guardian ta wallafa cewa gwamnatin Amurka ta ce manufar wannan sassauci shi ne samar da daidaito a kasuwar mai ta duniya, musamman bayan rikicin da ke faruwa tsakanin Amurka da Iran.
Sakataren baitul malin Amurka, Scott Bessent, ya ce matakin ba zai haifar wa gwamnatin Rasha da wani babban karin kudin shiga ba.
A cewarsa, yawancin kudin da Rasha ke samu daga makamashi suna fitowa ne daga harajin da ake karba yayin da ake hako mai.

Source: Getty Images
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana cewa duk wani mataki da zai sassauta takunkumi ga Rasha a wannan lokaci na iya kawo cikas ga kokarin da ake yi na takaita karfin tattalin arzikin Moscow.

Kara karanta wannan
Yadda yakin Iran da Amurka zai shafi ibadun watan Ramadan, Umrah da aikin Hajjin 2026
Ana sukar sassuta takunkumin Rasha
Shugaban Ukraine, Zelenskyy, ya soki matakin da Amurka ta dauka, yana mai cewa hakan na iya ba Moscow damar samun biliyoyin Daloli a kowane wata.
Ya kara da cewa irin wannan mataki ba zai taimaka wajen kawo karshen rikicin da ake yi ba tsakanin kasarsa da Rasha ba. A nata bangaren, kungiyar EU ta nuna cewa har yanzu ba ta da niyyar sassauta takunkumin da ta kakaba wa Rasha.
Shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz, ya ce rage takunkumi a wannan lokaci babban kuskure ne.
Har ila yau, wasu shugabannin Turai sun yi gargadin cewa duk wata barazana ga zirga-zirgar mai ta hormuz ba ta kamata ya zama dalilin sassauta takunkumi ga Rasha ba, domin hakan na iya sauya daidaiton siyasar makamashi a duniya.
Amurka ta harba bama-bamai Iran - Trump
A wani labarin, kun ji cewa Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya sanar da cewa ya kai mummunan hari tsibirin Kharg da ke kasar Iran bayan barazanar da ya yi.
Tsibirin Kharg daya ne daga cikin muhimman wuraren da daular Musulunci ta Iran ke hako danyen mai da ke zama ginshikin habaka tattalin arzikinta a yau.
Gwamnatin Iran ta fitar da gargadi game da ikirarin da shugaba Trump ya yi, ta ce za ta yi martani mai zafi a kan duk wani hari da aka kai mata nan ba da jima wa ba.
Asali: Legit.ng

