Masu Leken Asiri Sun Gano Abin da ba Zai Yiwa Amurka da Isra'ila Dadi ba kan Kasar Iran

Masu Leken Asiri Sun Gano Abin da ba Zai Yiwa Amurka da Isra'ila Dadi ba kan Kasar Iran

  • Hukumar leken asirin Amurka ta gano cewa har yanzu shugabannin Iran na nan daram kuma cikin hadin kai, babu alamar rushewar gwamnatin kasar
  • Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa masu bincike sun mika rahotanni daban-daban kuma duka sakamakon ya zama iri daya
  • A kwanakin baya, Shugaba Donald Trump da Firaministan Isra'ila sun bukaci al'ummar Iran su fito su yi zanga-zangar sauya gwamnatin kasarsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Washington DC - Rahoton hukumar leken asirin Amurka ya nuna cewa duk da shafe kwanaki 12 ana musayar wuta, har yanzu shugabancin kasar Iran na nan daram kuma babu alamar zai rushe.

Wannan rahoto dai ba zai yi wa shugaban Amurka, Donald Trump da Firaministan Isra'ila dadi ba, duba da yadda suka dage kan yunkurin sauya tsarin gwamnatin Iran.

Kara karanta wannan

Trump ya yi barazanar kai wa Iran harin da 'ba a taba ganin irin sa ba'

Mojtaba.
Jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei da marigayi mahaifinsa, Ayatollah Ali Khamenei Hoto: Kawnat Haju
Source: Twitter

A rahoton tashar Al-Jazeera, majiyoyin da suka san bayanan sirrin sun ce rahotanni da dama na leken asiri sun bayar da sakamako iri daya cewa har yanzu gwamnatin Iran na rike da iko da goyon bayan al’ummar kasar.

Shugabancin Iran na nan daram

Wata majiya ta ce rahoton baya-bayan nan an kammala hada shi ne a cikin kwanaki kadan da suka gabata.

Rahoton ya nuna cewa duk da kashe tsohon jagoran Iran, Ali Khamenei a ranar 28 ga Fabrairu, shugabannin addini da na siyasa a Tehran sun ci gaba da kasancewa cikin hadin kai.

Bayan mutuwarsa, majalisar malaman addini ta nada dansa, Mojtaba Khamenei, a matsayin sabon jagoran addini na kasar.

Rahotannin sun kuma nuna cewa rundunar juyin juya hali (IRGC), wacce babbar rundunar soja ce mai tasiri a Iran, har yanzu na da cikakken iko tare da shugabannin rikon kwarya da suka karbi mulki bayan mutuwar Khamenei.

Kara karanta wannan

Amurka da Isra'ila sun sha mamaki, an gano abin da Iran ke amfani da shi a musayar wuta

Ko da yake hare-haren Amurka da Isra’ila sun kashe manyan jami’ai da kwamandojin IRGC da dama, tsarin gwamnatin kasar ta Musulunci bai rushe ba.

Trump ya nemi a sauya gwamnatin Iran

Tun bayan fara yakin, gwamnatin Shugaba Donald Trump ta bayar da dalilai daban-daban kan dalilin hare-haren.

A farko, Trump ya bukaci al’ummar Iran da su tayar da tarzoma su karbe gwamnati, amma daga baya manyan jami’an gwamnatinsa sun musanta cewa manufar yakin ita ce kifar da gwamnatin Iran.

Netanyahu da Trump.
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu lokacin da ya kai wa Shugaba Donald Trump ziyara a Amurka Hoto: Joe Raedle
Source: UGC

Isra'ila ta fara karaya a yaki da Iran

Wani jami’in Isra’ila ya shaida wa Reuters cewa kasar ta fara nuna shakkun cewa yakin zai iya kawo karshen gwamnatin addini ta Iran.

Sai dai wata majiya ta kara da cewa Isra'ila ba ta da niyyar barin sauran sassan gwamnatin Iran su ci gaba da kasancewa yadda suke ba.

Majiyoyin sun ce kifar da gwamnatin Iran na iya bukatar hari ta kasa domin bai wa al’ummar kasar damar fita zanga-zanga cikin aminci.

Iran ta sake lalata na'urar kariya ta Amurka

A baya, rahotanni sun ce Iran ta lalata wata na’ura mai kakkabo makamai mallakin Amurka mai darajar miliyoyin daloli a wani sansanin soja a Jordan.

Kara karanta wannan

Tsautsayi ya gitta, harin kasar Iran ya rutsa da 'dan Najeriya da wasu mutane sama da 100

An ce na'urar AN/TPY-2 mai darajar dala miliyan 300 na cikin tsarin kare makamai na THAAD da Amurka ke amfani da shi domin gano makamai masu linzami daga nesa.

Wani jami’in Amurka ya tabbatar da lalacewar na’urar, bayan rahotanni sun ce Iran ta kai hare-hare biyu a Jordan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262