Bidiyon Lokacin da Makamin Iran Ya Fada tsakiyar Birnin Isra'ila, Mutane Sun Mutu
- Sababbin hare-haren makaman linzami daga kasar Iran sun girgiza birnin Tel Aviv inda mutane biyu suka mutu wasu da dama kuma suka jikkata
- Ita ma kungiyar Hezbollah ta doki wata makarantar renon yara a Isra'ila inda mutane 14 suka jikkata yayin da ake tsaka da fafata wannan yaki
- Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa babban burin wannan yakin shi ne kawo ƙarshen mulkin Jamhuriyar Musulunci gaba ɗaya a kasar Iran
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Isra'ila - Tsakiyar kasar Isra'ila ta girgiza sakamakon wasu manyan fashe-fashe bayan da saukar makamai masu linzami da Iran ta harba zuwa birnin Tel Aviv da garuruwan dake makwabtaka da shi.
Hotuna da bidiyo daga yankin Bnei Brak sun nuna yadda baƙin hayaki ya mamaye sararin samaniya, tare da motocin da suka kife a kan titi sakamakon karfin fashewar.

Source: Getty Images
Isra'ila ta girgiza bayan saukar makaman Iran
Hukumomi sun bayyana cewa akwai wurare da dama da makaman suka fada, inda ake zargin cewa an samu makami guda ɗaya da yake ɗauke da bama-bamai masu rarrabuwa idan ya kusa sauka, in ji rahoton Time of India.
Jami'an agajin gaggawa na Magen David Adom sun garzaya wuraren da abin ya shafa, inda suka tabbatar da cewa aƙalla mutane shida ne suka jikkata.
Daga cikinsu har da wani mutum mai shekaru kusan 40 da ya samu rauni mai tsanani a Tel Aviv, yayin da wasu suka jikkata a Petah Tikva.
Wani bidiyo da kafar labaran Aljazeera ta wallafa shafinta na YouTube ya nuna daidai lokacin da wani makami ya daki tsakiyar Isra'ila, harin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu tare da jikkata wasu.
Kalli bidiyon a kasa:
Hare-haren Hezbollah kan Isra'ila
Bayan sa'o'i kadan da harin Iran, ƙungiyar Hezbollah ta harba nata makaman wadanda suka daki tsakiyar Isra'ila, inda suka jikkata mutane 16 tare da lalata wata makarantar rainon yara.

Kara karanta wannan
To fa: Musayar wutar da ake tsakanin Amurka, Isra'ila da Iran ta shiga wani muhimmin mataki
A garin Ramle, jami'an agaji sun kula da mutane 14 da suka samu raunuka marasa tsanani. Haka kuma, Hezbollah ta sanar da cewa ta kai harin jirage marasa matuƙi kan sansanin sojin Isra'ila na "Samson" (wanda aka fi sani da Camp Shimshon) dake yammacin tekun Galili.
Duk da cewa gwamnatin Trump na nuna cewa yaƙin zai kasance na ɗan gajeren lokaci, ra'ayin Firayim Minista Benjamin Netanyahu ya bambanta sosai da na shi.
Yadda Isra'ila take kallon yaki da Iran
Netanyahu ya bayyana sarai cewa manufarsa ba kawai raunata Iran ba ce, a'a, manufar ita ce samar da yanayin da zai kawo ƙarshen mulkin Jamhuriyar Musulunci gaba ɗaya domin maye gurbinsa da gwamnati mai abota da Isra'ila.
Jami'an Isra'ila na kallon wannan yaƙin a matsayin "dama ta musamman" da ba za su bari ta kuɓuce musu ba.
Suna jaddada cewa ba za su sassauta ba muddin Amurka a shirye take ta ci gaba da ba su goyon baya a wannan fafatawa, in ji rahoton The Times of Israel.
Gargaɗin da suke yi wa jama'a shi ne cewa wannan yaƙin zai ɗauki duk tsawon lokacin da ya kamata har sai an cimma nasara, lamarin da ke nuna cewa rikicin na iya tsawaita fiye da yadda wasu ke tsammani yau.

Kara karanta wannan
Luguden wutar Amurka da Isra'ila ya yi barna a kasar Musulunci ta Iran, sama da mutum 100 sun mutu
Dabarun Iran na yanzu sun fi na baya
Wannan sabon yaki ya nuna cewa dabarun Iran na wannan karon sun fi na baya tsanani, musamman ma ganin yadda za su yi yakin don fanshe kisan jagoransu.
Wani dan Najeriya mazaunin Kuwait, Sadiq Madabo, ya shaida wa Legit Hausa cewa, su da suke a Gabas ta Tsakiya, sun gaskata karin karfin Iran.
Sadiq Madabo ya ce wannan yakin ya zo da sabon salo, domin kuwa shirin da Iran ta yi wannan karon ya fi wanda ta yi a shekarar baya, don haka ba kanwar lasa ba ce.
"A yanzu na ga hakikanin karfin Iran, domin kan ka ce me, sun kai hare-hare a kasashe bakwai na Larabawa. Amma ina rokon Allah ya takaita, don idan ya wuce haka, to wasu kasashe za su iya shiga."
- Sadiq Madabo.
Sanatan Amurka yana kokarin rura wutar yaki
A farkon makon nan ne labari ya zo cewa Sanata a jam'iyya mai rinjaye a majalisar Amurka, Lindsay Graham ya dura a kan ƙasashen Larabawa kan yaki da Iran.
Lindsay Graham ya yi masu gori bayan sun ki shiga a hadu da Isra'ila wajen yaƙar Iran. Sanatan ya bayar ba Larabawa shawarar su yi wa Iran taron gangi.
Hakan na zuwa ne bayan an rika samun labaran cewa dakarun Iran sun karyata rahotannin kai hare-haren da sunansu a kasashen Turkiyya da Saudi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

