Amurka Ta Fara Karaya ne? Trump Ya Faɗi Abin da ba a Sani ba game da Iran
- Shugaban Amurka Donald Trump ya yi magana kan ƙarfin da Iran ke da shi yayin da ake ci gaba da yaki a Gabas ta Tsakiya
- Trump ya ce Iran na da makamai masu linzami fiye da yadda aka zata, yana zargin cewa kasar na shirin kai hari kan Amurka
- Shugaban ya ce bayan mako guda Iran za ta kai hari, yana mai cewa suna da makamai masu linzami da dama fiye da yadda mutane suka yi tunani
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana karfin makamai da Iran ke da shi a yanzu.
Trump ya bayyana cewa Iran na da makamai masu linzami da yawa fiye da yadda aka zata, inda ya ce kasar ta shirya kai hari kan Amurka.

Source: Twitter
Yadda Iran ta shirya kai hari Amurka
Trump ya yi wannan bayani ne yayin da yake jawabi ga ‘yan jam’iyyar Republican a wani taron manufofi na shekara da aka gudanar a jihar Florida, cewar Al Jazeera.
Ya ce:
“Zan ba ku mafi kyawun misali, cikin mako guda suna shirin kai mana hari, kashi 100 cikin 100. Sun shirya gaba daya.”
Trump ya kara da cewa Iran na da makamai masu linzami da yawa fiye da yadda aka taba tsammani, kuma suna shirin amfani da su ke wajen kai hari.
Maganganun nasa sun zo ne a daidai lokacin da Amurka ke ci gaba da yakin soji da Iran, wanda Trump ya ce yana dab da karewa.
A wata hira ta waya da kafar CBS News, Trump ya ce sojojin Amurka sun riga sun raunana karfin sojin Iran sosai.
Ya ce:
“Ina ganin yakin ya kusan karewa gaba daya. Iran ba ta da rundunar ruwa, ba ta da sadarwar soja, kuma ba ta da rundunar sama.”

Source: Twitter
Amurka ta magantu kan makamai masu linzamin Iran
Trump ya kara da cewa makaman linzamin Iran sun ragu sosai, yayin da jirage marasa matuki da suke kera wa ke lalacewa a wurare daban-daban.
A cewar rundunar sojin Amurka, an kai hare-hare kan wurare sama da 3,000 a fadin Iran a cikin makon farko na wannan farmaki.
Trump ya ce:
“Idan kuka duba, babu abin da ya rage musu. A bangaren soja, babu wani karfi da ya rage.”
A karshe mako, Iran ta sanar da cewa Mojtaba Khamenei zai gaji mahaifinsa a matsayin jagoran koli na kasar, cewar Punch.
Sai dai Trump ya ce ba shi da wani sako gare shi, yana mai cewa yana da wani mutum daban a zuciyarsa wanda zai jagoranci Iran a gaba.
Iran ta harba makamai cikin Saudiyya
A wani labarin rahoto ya nuna cewa ma’aikatar tsaron kasar Saudiyya ta ce sojoji sun harbo jirage marasa matuƙa da suka nufi matatar mai.
Ta bayyana cewa ta yi nasarar harbo jiragen daga sama, amma duk da haka an ce karafun jiragen sun haddasa gobara a matatar man.
Matatar Ras Tanura da ke kusa da Dammam na iya tace fiye da gangar mai rabi miliyan a rana daya, tana cikin mafi girma a Gabas ta Tsakiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


