Yadda Yakin Amurka da Iran Ya Jefa Gwamnatin Donald Trump a Fargaba
- Tasirin da yakin Amurka/Isra'ila da Iran ya ke haifarwa a bangaren makamashi ya fara jefa fargaba a gwamnatin shugaba Donald Trump
- Jami'an gwamnatin Trump sun yi zama a karshen makon da ya wuce domin sake nazari game da hanyar da za su shawo kan lamarin
- Tun bayan kashe Ayatollah Ali Khamenei, hukumomin Iran suka rufe mashigar Hormuz da ake bi wajen jigilar mai zuwa kasashe duniya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Gwamnatin shugaba Donald Trump ta fara nuna fargaba kan yadda farashin mai ke tashi cikin sauri a kasuwannin duniya.
Hakan na zuwa bayan shafe sama da mako daya ana gwabza yaki tsakanin Iran da Amurka/Isra'ila, lamarin da ya shafi kasashe da dama a masu samar da mai a Gabas ta Tsakiya.

Source: Getty Images
Rahoton CNN ya nuna cewa wasu jami'an gwamnatin Trump sun shafe sa'o'i suna tattauna hanyoyin da za a warware matsalolin da suka taso.
Hasashen Donald Trump kan yaki da Iran
Manyan masu ba shugaba Trump shawara sun yi hasashen cewa za a iya samun tashin farashin mai kadan a kwanakin farko na yakin da ake yi da Iran.
Sai dai tashin farashi sosai da kuma yadda yake ci gaba da yin zama ba tare da sauka ba ya ba su mamaki, kamar yadda wasu da suke da alaka da lamarin suka bayyana.
Korafin da ake yi game da Trump
The Guardian ta rahoto cewa tashin farashi ya sa gwamnatin Trump ta fara kokarin kwantar da hankalin masu zuba jari tare da neman hanyoyin rage tasirin tsadar mai.
Duk da haka, gwamnatin na fuskantar kalubale, inda wasu ke cewa shiga yaki da shugaba Trump ya yi na iya lalata wasu manyan nasarorin tattalin arziki da ya samu.
Wani gogaggen masani kan harkokin makamashi kuma tsohon shugaban sashen masana’antar mai da kasuwanni na Hukumar Makamashi ta Duniya, Neil Atkinson ya ce yana da wuya farashin ya daina tashi.
Ya ce:
“Yana da wuya a samu sauki face karin farashi. Mutane za su dandana hakan a gidajen mai.”
A halin yanzu, zirga-zirgar jiragen dakon mai ta mashigar Hormuz ta kusan tsayawa cak, lamarin da ya kawo cikas ga kusan kashi 20 cikin 100 na man da ake samarwa a duniya.

Source: Getty Images
A ranar Litinin, farashin mai ya kusa kaiwa $120 kan kowace ganga kafin daga baya ya dan sauka kadan. Wannan mataki ne da ba a gani ba tun farkon yakin Rasha da Ukraine a shekarar 2022.
Gwamnatin Donald Trump na cikin fargaba
Tashin farashin ya tayar da hankalin jami’ai a gwamnatin Trump, wadanda tun farko suka shirya yin amfani da saukar farashin mai a matsayin daya daga cikin manyan ginshikan yakin neman zaben jam’iyyar Republican Nuwamban 2026.
A cewar wasu da suka san lamarin, wannan damuwa ta karu sosai a karshen mako bayan farashin mai ya kai $100 kan kowace ganga.
An kuma bayyana cewa matakan farko da gwamnatin ta dauka sun kasa rage fargabar da ake yi game da yiwuwar barkewar rikicin makamashi a duniya.
Tashin farashin mai ya shafi Najeriya
A tattaunawa da wani mai aiki da babban motar dakon yashi, Musa Yusuf, ya bayyanawa Legit Hausa cewa farashin man dizil ya tashi sosai:
"A yanzu haka mun samu kari sosai. Kayan da muke daukowa a N60,000 yanzu zai kai kusan N90,000 ko N100,000."
"Muna fatan wannan yakin ya tsaya haka domin samun sauki, a yanzu masu mai ne kawai ke cin riba sosai ba masu wahalar loda kaya ko tuki ba."
Trump ya magantu kan yaki da Iran
A wani labarin, kun ji cewa Shugaban Amurka, Donald Trump ya sake magana kan shirin kawo karshen yakin da ya kaddamar a Iran.
Hakan na zuwa ne yayin da aka shafe kwana 10 ana fafatawa a fagen daga, lamarin da ya jawo asarar rayuka bayan yakin ya shafi kasashe da dama.
Trump ya bayyana cewa nan gaba kadan za a kawo karshen yakin, duk da cewa bai ayyana ainihin lokacin da za a daina kai hare-hare ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


