Mojtaba: Babban Basarake a Najeriya Ya Tura Muhimmin Sako ga Sabon Jagoran Iran

Mojtaba: Babban Basarake a Najeriya Ya Tura Muhimmin Sako ga Sabon Jagoran Iran

  • Babban basarake a Najeriya, Oba Abdulrosheed Akanbi, ya yi magana kan nadin da aka yi wa Mojtaba Khamenei, a matsayin sabon jagoran addini na kasar Iran
  • Basaraken mai rike da sarautar Oluwo na Iwo ya bayyana cewa nadin Mojtaba ya zo ne a lokaci mai muhimmanci kuma mai cike da hadari
  • Oba Abdulrosheed Akanbi ya bayyana cewa ba za a iya mancewa da radadin kisan gillar da aka yi wa mahaifin Mojtaba Khamenei ba

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Osun - Oluwo na Iwo, Oba Abdulrosheed Akanbi, ya aika sako ga sabon jagoran addinin kasar Iran, Mojtaba Khamenei.

Oluwo na Iwo ya taya Mojtaba Khamenei murnar samun kujerar, inda ya bayyana cewa ya karɓi ragamar shugabancin ne a wani lokaci mai matuƙar muhimmanci da haɗari.

Oluwo na Iwo ya ba Mojtaba Khamenei shawara
Sabon jagoran addini na kasar Iran, Mojtaba Khamenei Hoto: Reza B
Source: Getty Images

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa babban basaraken ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa a ranar Litinin, 9 ga watan Maris 2026.

Kara karanta wannan

China ta shata wa Amurka da Isra'ila layi kan sabon jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei

Me basaraken ya gayawa Mojtaba Khamenei?

Oluwo ya shaidawa sabon jagoran na Iran cewa yana da damar da zai samar da zaman lafiya ko akasin haka.

“Kwarewar ka wajen gudanar da mulki za ta zama silar zaman lafiyar duniya ko akasin haka. Duniya tana nishi cikin raɗaɗi, yankin Gabas ta Tsakiya kuma yana zubar da jini sosai."
"Ba za a iya mancewa da raɗaɗin kisan gilla da aka yi wa tsohon jagora Iran, Ayatollah Ali Khamenei ba, amma ba za a taɓa samun zaman lafiya ba idan muka ƙi yafe wa kanmu. Tuni tattalin arziki ya ruguje."
"Talakawa suna shan wahala sosai wajen samun abinci. Farashin man fetur ya tashi sama, kuma yana neman ya gagari talaka. Radadin tattalin arziki ya zama abin da ba za a iya jurewa ba."
“Ina roƙonka da ka bi hanyar yafiya domin ceto mutanen da ba su ji ba ba su gani ba daga wannan wahala da za a iya kauce mata. Idan yaƙin nan ya ci gaba, mutane masu ƙaramin ƙarfi za su ƙare saboda yunwa."

Kara karanta wannan

Ana cikin musayar wuta, Shugaba Putin ya aika sako ga sabon jagoran Iran, Mojtaba Khamenei

Oba Abdulrosheed Akanbi

Oluwo ya bukaci Mojtaba ya rungumi zaman lafiya

Babban basaraken ya bukaci sabon jagoran na Iran da ya rungumi hanyar tattaunawa domin ganin an kawo karshen rikicin, jaridar The Sun ta kawo labarin.

Oluwo na Iwo ya yi magana kan sabon jagoran addinin kasar Iran
Oluwo na Iwo, Oba Abdulrosheed Akanbi Hoto: Taofeek Adeniyi
Source: Facebook
“Amincewa da tattaunawa ba tsoro ba ne. Waɗanda suka rungumi zaman lafiya su ne ainihin waɗanda suka yi nasara. Ya kamata hukumomin Amurka da shugabannin Isra'ila su yi kiran tsagaita buɗe wuta."
"Kayan more rayuwa da aka gina na tsawon shekaru da dukiyar masu biyan haraji duk an lalata su kuma an goge su."
“Idan Mojtaba Khamenei ya ce 'eh' ga zaman lafiya a yau, duniya za ta zauna lafiya. Ina da kyakkyawan fata cewa za a tuna da gwamnatinka wajen maido da zaman lafiya, aminci da arziki ga duniya.”

- Oba Abdulrosheed Akanbi

Trump ya magantu kan sabon jagoran Iran

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi magana kan sabon jagoran da zai jagoranci kasar Iran.

Kara karanta wannan

Mojtaba Khamenei: Iran ta zabi sabon jagora da zai kalubalanci Trump da Isra'ila

Donald Trump ya bayyana cewa sabon jagoran da zai jagoranci Iran, Mojtaba Khamenei ba zai daɗe yana kan mulki ba.

Shugaban na Amurka ya bayyana cewa matukar aka tabbatar da sabon shugaban ba tare da ya samu sahalewar Amurka ba, an yi aikin kawai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng