Hezbollah Ta Kakkabo Jirgin Yaƙin Isra'ila, an Kashe fiye da Mutane 1330 a Iran
- Hezbollah ta kakkabo jirgin yakin Isra'ila a gabashin Lebanon yayin da dakarun commando suka yi kokarin mamaye garin Nabi Sheet
- Harin Isra'ila kan wata makarantar firamare ta yan mata a birnin Minab na kasar Iran ya yi sanadiyyar mutuwar kananan yara 180
- Akalla mutane 1,332 ne suka riga mu gidan gaskiya a Iran sakamakon hare-haren hadin gwiwar Amurka da Isra'ila da ya shiga rana ta 10
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Lebanon - Ƙasar Lebanon ta tsinci kanta a cikin guguwar yaƙin yankin Gabas ta Tsakiya a makon da ya gabata, bayan da ƙungiyar Hezbollah mai samun goyon bayan Iran ta kai hari kan Isra'ila.
Wannan mataki ya biyo bayan kisan babban jagoran Iran, Ayatollah Ali Khamenei, a hare-haren haɗin gwiwar sojojin Amurka da Isra'ila.

Source: Getty Images
Dakarun Hezbollah na fafatawa da Isra'ila
Duk da cewa akwai yarjejeniyar tsagaita wuta ta shekarar 2024, Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare kan Hezbollah, inda a makon jiya ta tura dakarun ƙasa zuwa yankunan kan iyaka, in ji rahoton RFI.
A cikin wata sanarwa da ta fitar yau Litinin, Hezbollah ta bayyana cewa ta gano "shigar kusan jirage masu saukar ungulu 15 na abokan gaba" daga ɓangaren iyakar Siriya zuwa gabashin Lebanon.
Ƙungiyar ta ce dakarunta sun yi artabu da jiragen da kuma sojojin da suka shigo da "makamani," kuma har yanzu ana tsaka da fafatawar.
Kamfanin dillancin labarai na Lebanon (NNA) ya ba da rahoton "kazamin faɗa" a kewayen garin Nabi Sheet, inda Hezbollah ke kokarin fatattakar sojojin na Isra'ilan.
Hezbollah ta kakkabo jirgin Isra'ila
Wasu jami'an Hezbollah guda biyu a yankin Bekaa sun tabbatar wa manema labarai cewa an yi nasarar kakkabo jirgi mai saukar ungulu guda ɗaya na Isra'ila, in ji rahoton Asharq Al-awsat.

Kara karanta wannan
Bakin hayaki ya turnuke Tehran, Amurka ta yi wa Iran mummunar barna a karon farko
Wannan shi ne hari na biyu makamancinsa bayan wani yunƙuri na dakarun commando na Isra'ila a garin Nabi Sheet a daren Juma'a ya ci tura, inda sojojin suka gaza nemo gawar matuƙin jirgin nan Ron Arad da ya ɓace tun 1986, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 41.
A babban birnin Lebanon, Beirut, an ji ƙarar wani babban fashewa a yau Litinin a kudancin birnin wanda ke matsayin sansanin Hezbollah.
Wannan farmaki ya zo ne bayan kwanaki biyu da daina kai hare-hare a yankin, kodayake Isra'ila ta riga ta gargaɗi mazauna yankin da su kwashe kayansu tun da wuri yau.
Asarar rayuka: Mutuwar mutane 1332 a Iran
Yayin da yaƙin ya shiga rana ta 10, asarar rayuka na ci gaba da ƙaruwa a ƙasashe 12 da yaƙin ya shafa, kamar yadda rahoton Aljazeera ya nuna.

Source: Getty Images
A Iran, adadin waɗanda suka mutu ya tashi zuwa 1,332, inda babban abin alhinin ya faru a birnin Minab. Harin da Isra'ila ta kai wata makarantar firamare ta ƴan mata a birnin ya yi sanadiyyar mutuwar "ƙananan yara kusan 180," a cewar ma'aikatar lafiyar Iran.
A Lebanon kuma, Ministan Lafiya ya bayyana cewa hare-haren Isra'ila sun kashe mutane 394 a cikin mako guda, ciki har da yara 83.
A ɓangaren Isra'ila, rundunar sojin ƙasar ta tabbatar da mutuwar sojojinta guda biyu a fafatawar dake gudana a kudancin Lebanon.
Wannan yaƙi ya jefa yankin cikin mummunan hali, yayin da Tehran ke ci gaba da mayar da martani da makaman linzami da jirage marasa matuƙi kan sansanonin Amurka da Isra'ila.
Isra'ila ta farmaki Hezbollah a Lebanon
Kun dai ji cewa, Isra’ila ta sake kaddamar da hare-hare a kudancin Lebanon, inda ta yunkurin kashe wasu kwamandojin rundunar Quds ta dakarun juyin juya halin Iran.
Wannan harin ya biyo bayan furucin Benjamin Netanyahu, wanda ya yi alkawarin cewa za a ga “abubuwan mamaki da dama” a mataki na gaba na yakin da ke gudana.
A cikin wata sanarwa, sojojin Isra’ila sun bayyana cewa ba za su bari “kungiyoyin ta’addanci na Iran su kafa sansani a cikin kasar Lebanon ba."
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

