Hare Haren Iran Sun Sake Ajalin Sojan Amurka a Kasar Saudiyya
- Rahotanni sun nuna cewa an sanar da mutuwar wani sojon Amurka a kasar Saudiyya bayan makaman da Iran ta harba sun masa mummunar illa
- Rundunar sojojin Amurka ta sanar da cewa a ranar 1 ga watan Maris 2026 ne Iran ta kaddamar da hare-hare kan sansanin da suke zaune
- An sanar da mutuwar sojan ne 'yan sa'o'i bayan Donald Trump ya karbi gawar wasu dakarun sojojin Amurka shida da Iran ta kashe a Kuwait
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Saudi Arabia - Amurka na cigaba da rasa dakaru a yakin da ta hada kai da Isra'ila suka kaddamar a kasar Iran a ranar 28 ga Fabrairun 2026.
An sanar da mutuwar wani soja a Saudiyya bayan an mayar da sojojin Amurka shiga da suka rasu a Kuwait a harin da Iran ta kai musu.

Source: Getty Images
Rundunar sojin Amurka a Gabas ta Tsakiya ce ta sanar da rasuwar sojan a wani sako da ta wallafa a shafinta na X a ranar Lahadi, 8 ga Maris, 2026.
Sojan Amurka ya mutu a yaki da Iran
Sojan Amurka guda daya ya mutu bayan ya samu munanan raunuka a wani hari da aka kai makon da ya gabata a kasar Saudiyya.
Tashar CNN ta rahoto cewa rundunar sojin Amurka ta bayyana cewa mutuwar sojan ya kawo adadin sojojin Amurka da suka mutu a yaki da Iran zuwa bakwai.
“A daren jiya, wani sojan Amurka ya rasu sakamakon raunukan da ya samu yayin hare-haren farko na gwamnatin Iran a yankin Gabas ta Tsakiya,”
Inji rundunar sojin Amurka.
Dakarun Amurka sun kara da cewa:
“Sojan ya samu mummunan rauni a wurin wani hari da aka kai kan sojojin Amurka a Saudiyya a ranar 1 ga Maris.”
Sai dai duk da sanar da rasuwarsa, ba a bayyana sunan sojan ba har sai bayan sa'o'i 24 da sanar da iyalansa, kamar yadda dokar Amurka ta tanada.
Sojojin Amurka 6 sun rasu a Kuwait
Labarin mutuwar wannan soja ya zo ne kwana guda bayan bikin karɓar gawar sojoji shida da aka kashe makon da ya gabata a Kuwait.
Shugaban Amurka Donald Trump tare da wasu manyan jami’ai sun halarci taron tare da iyalan sojojin a sansanin sojin sama na Dover a jihar Delaware yayin da aka dawo da gawar sojojin gida.

Source: Twitter
Dama dai Trump ya taba cewa a baya ana iya samun karin asarar rayukan sojojin Amurka a wannan yakin da suka kaddamar a kan Iran.
Da aka tambaye shi ko yana ganin zai sake halartar irin wadannan bukukuwan karɓar gawar sojoji, Trump ya ce:
“Ina da tabbaci. Bana so… amma wannan bangare ne na yaki.”
Trump ya yi maganar tsayar da yaki
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban Amurka, Donald Trump ya yi magana kan yiwuwar tsayar da yaki da Iran bayan shiga mako na biyu.
Ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi, inda ya ce zai tattauna da Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu kafin yanke matsaya.
Trump ya kara da cewa ba ya tunanin Isra'ila za ta cigaba da kai hari Iran bayan ya dakatar da yakin da aka fara a karshen watan Fabrairun 2026.
Asali: Legit.ng


