Fetur Ya Kara Tsada: Yadda Yakin Iran Ya Jawo Farashin Gangar Mai Ya Haura $100

Fetur Ya Kara Tsada: Yadda Yakin Iran Ya Jawo Farashin Gangar Mai Ya Haura $100

  • Farashin danyen mai ya haura dala 100 a kasuwannin duniya sakamakon yakin da ake gwabzawa tsakanin Amurka/Isra'ila da kasar Iran
  • Shugaba Donald Trump ya bayyana tsadar man a matsayin dan takaitaccen kalubale da duniya za ta fuskanta yayin da Amurka ke yaki da Iran
  • Kasuwannin hannun jari na duniya sun fuskanci faduwar daraja yayin da Iran ta yi barazanar cewa farashin man zai iya kai dala 200

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Iran - Farashin gangar ɗanyen mai na duniya ya haura $100 a karon farko tun shekarar 2022, yayin da yaƙin Amurka/Isra'ila da ƙasar Iran ya ke salwantar da gangar mai miliyan 20 a kowace rana.

Hare-haren da aka kai wa rumbunan ajiyar mai biyar a birnin Tehran a ƙarshen mako ya tsoratar da masu zuba jari, wanda hakan ya sa farashin man ya tashi zuwa mataki mafi girma cikin shekaru huɗu.

Kara karanta wannan

Trump na tsakiyar yaki da Iran: Bam ya tarwatse a wani ofishin jakadancin Amurka

An samu tashin farashin gangar danyen mai zuwa sama da $100 karon farko tun 2022
Wasu motocin dakon mai da suka babbake a kusa da rumbunan ajiyar fetur da harin Amurka ya tarwatsa a Tehran. Hoto: Hassan Ghaedi/Anadolu via Getty Images
Source: Getty Images

Yakin Iran: Farashin mai ya haura $100

Brent Crude, wanda shi ne ma'aunin farashin mai na duniya, ya yi tashi da 26.3% inda ya kai dala 117.08, yayin da danyen man Amurka (WTI) ya tashi da 28.7% zuwa dala 119.96, in ji rahoton Aljazeera.

Wannan tashin gwauron zabon na zuwa ne sakamakon rufe mashigar ruwa ta Hormuz — wadda kusan kashi ɗaya bisa biyar na man fetur ɗin duniya ke bi ta cikinta.

"Tattalin arzikin duniya ya dogara ne kan safarar mai da iskar gas daga Gabas ta Tsakiya ta mashigar ruwan Hormuz," in ji Bruce Kasman, babban masanin tattalin arziki a JPMorgan.

Ya shaidawa kafar labaran Reuters cewa:

"Farashin danyen man na iya haura $120 la'akari da yadda yakin yake tafiya. Amma idan aka samu wata maslaha, to man Brent zai sauka zuwa $80 zuwa tsakiyar shekara.

Ya kuma yi gargadin cewa idan wannan yakin ya ci gaba da fadada, to farashin gangar danyen mai za ta haura $120 kuma duniya na iya fuskantar durkushewar tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Bakin hayaki ya turnuke Tehran, Amurka ta yi wa Iran mummunar barna a karon farko

Martanin Trump kan tsadar danyen mai

Duk da wannan tsadar mai da take barazana ga tattalin arziki, Shugaba Donald Trump ya bayyana cewa wannan "ƙaramin farashi ne" da ya kamata Amurka da duniya su fuskanta a kokarin samar da zaman lafiya mai ɗorewa.

Trump ya yi iƙirarin cewa farashin zai faɗi ƙasa cikin sauri da zarar an gama murƙushe barazanar nukiliyar Iran, in ji rahoton The Guardian.

Sai dai dakarun kare juyin juya hali na Iran (IRGC) sun yi gargaɗin cewa idan har ba a daina wannan yaƙin ba, farashin gangar man na iya haura dala 200.

Farashin danyen mai ya haura $100 a kan kowace ganga
Farashin man fetur da gas a wani gidan mai a Barcelona, Catalonia, Spain. Hoto: David Zorrakino/Europa Press via Getty Images
Source: Getty Images

Kasuwannin hannun jari sun fadi

Kasuwannin hannun jari a ƙasashen Japan, Koriya ta Kudu, da Australia duk sun fuskanci faɗuwar daraja a safiyar yau Litinin, yayin da ake cikin wannan yaki.

Masu sharhi kan makamashi sun bayyana cewa giɓin gangar mai miliyan 20 a kowace rana babban ƙalubale ne ga duniya, musamman ganin yadda Trump ya buƙaci Iran ta miƙa wuya gaba ɗaya, lamarin da ake ganin ba zai faru cikin sauƙi ba.

Kara karanta wannan

Iran ta gamu da gagarumar matsala tana tsakiyar musayar wuta da Amurka/Isra'ila

Sakataren makamashi na Amurka, Chris Wright, ya yi ƙoƙarin kwantar wa masu zuba jari hankali inda ya ce wannan matsalar ba za ta wuce ta makonni ba.

Farashin fetur ya tashi a Najeriya

A wani labari, mun ruwaito cewa, yakin da ake yi a yankin Gabas ta Tsakiya ya fara shafar wasu sassa na duniya dangane da farashin man fetur.

A Najeriya, farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabi a birnin Legas bayan matatar Dangote ta kara kudi kan yadda take sayarwa 'yan kasuwa.

A yanzu farashin man fetur yana tsakanin N1,020 zuwa N1,080 kan kowace lita, amma ya danganta ne da wurin da gidan man yake.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com