Mojtaba Khamenei: Iran Ta Zabi Sabon Jagora da Zai Kalubalanci Trump da Isra'ila

Mojtaba Khamenei: Iran Ta Zabi Sabon Jagora da Zai Kalubalanci Trump da Isra'ila

  • An nada Mojtaba Khamenei a matsayin sabon jagoran addini na Iran don maye gurbin mahaifinsa wanda Amurka da Isra'ila suka kashe
  • Zaben Mojtaba ya nuna cewa kasar Iran ta zabi hanyar yaki da daukar fansa maimakon sulhu da Shugaba Donald Trump da Isra'ila
  • Dakarun IRGC za su samu karin iko a karkashin sabon jagoran yayin da ake fargabar 'yan Iran za su kara fuskantar tsananin rayuwa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Iran - A wani mataki na nuna turjiya da rashin mika wuya, majalisar kwararru ta kasar Iran ta nada Mojtaba Khamenei a matsayin sabon jagoran addini na kasar.

Mojtaba Khamenei ya gaji mahaifinsa, Ayatollah Ali Khamenei, wanda aka kashe a wani harin hadin gwiwa na Amurka da Isra'ila a makon jiya.

Iran ta nada Mojtaba Khamenei a matsayin sabon jagoran addinin kasar
Majalisar kwararru ta Iran ta nada Mojtaba Khamenei (dama) a matsayin sabon jagoran addinin kasar a Tehran. Hoto: Iranian President's Press Office / Handout /Anadolu via Getty Images)
Source: UGC

Iran ta zabi sabon jagoran addini

Kara karanta wannan

Ana tsakiyar musayar wuta, an zabi wanda zai zama sabon jagoran addini a Iran

Wannan nadi ya zo ne a matsayin kakkausan raddi ga Shugaban Amurka Donald Trump, wanda tun farko ya ce Iran ba za ta nada jagora ba tare da amincewarsa ba, in ji rahoton Reuters.

Masu sharhi kan al'amuran yau da kullum na ganin cewa zabar Mojtaba, mai shekaru 56, wanda aka sani da tsautstsauran ra'ayi, sako ne karara cewa Iran ta yi watsi da duk wata hanyar sulhu.

Mojtaba ba bako ba ne a cikin tsarin ikon kasar, domin ya dade yana aiki a matsayin "mai gadin kofa" na mahaifinsa, inda ya gina dangantaka mai karfi da dakarun kare juyin juya hali (IRGC).

Ana sa ran Mojtaba zai jagoranci kasar cikin azama, inda zai bayar da fiffiko ga sojoji domin daukar fansa kan kisan mahaifinsa da sauran danginsa da aka kashe a hare-haren kwanan nan.

Kalubale ga sabon jagoran Iran

Mojtaba Khamenei na karbar ragamar mulki ne a daidai lokacin da kasar Iran ke fama da karyewar tattalin arziki, tashin gwauron zabon farashin kayayyaki, da kuma fargabar boren jama'a a cikin gida.

Majiyoyi daga birnin Tehran sun bayyana cewa wannan yaki da ake kan yi zai jefa Iran cikin wahalar rayuwa nan gaba, yayin da ake ganin Mojtaba ba zai taba amincewa da tattaunawa da kasashen Yamma ba.

Kara karanta wannan

Iran ta gamu da gagarumar matsala tana tsakiyar musayar wuta da Amurka/Isra'ila

Wannan zai iya haifar da karin matsin lamba ga al'ummar kasar wadanda dama can suke cikin kunci kafin ma barkewar wannan yakin, cewar rahoton The Guardian.

Mojtaba Khamenei zai fuskanci Amurka da Isra'ila a matsayin sabon jagoran addini na Iran.
Mojtaba Khamenei (tsakiya), d'a ga Ayatollah Ali Khamenei, wanda yanzu ya zama jagoran addinin Iran. Hoto: Morteza Nikoubazl/NurPhoto via Getty Images
Source: Getty Images

Fuskantar barazanar Trump da Isra'ila

A daya bangaren kuma, Isra'ila ta riga ta yi gargadin cewa dukkan wanda ya gaji Khamenei zai zama abun farmaki ga dakarunsu.

Wannan nadi ya sanya yankin Gabas ta Tsakiya a cikin wani hali na dar-dar, inda ake fargabar cewa Mojtaba zai kara tsananta hare-haren makami mai linzami da jirage mara matuki zuwa kasashen dake makwabtaka da Iran domin nuna cewa yana da ikon kare kasarsa.

Abin da zai kawo karshen yakin Iran

A wani labari, mun ruwaito cewa, shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya yi magana game da abin da zai kawo karshen yakin Iran da Isra'ila.

Trump ya bayyana cewa yaƙin da ke gudana a Gabas ta Tsakiya na iya ƙarewa ne kawai idan an lalata shugabancin Iran da kuma rundunar sojinta gaba ɗaya.

A baya-bayan nan dai Trump ya bukaci Iran ta mika wuya ba tare da wani sharadi ba, lamarin da ya sa shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya mayar da martani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com