Trump Ya Tona Ƙullin a Suke Yi wa Sabon Jagoran Addini na Iran
- Shugaban Amurka Donald Trump ya ce sabon jagoran Iran ba zai daɗe a mulki ba idan bai samu amincewar Amurka ba
- Trump ya yi zargin cewa Iran na shirin mamaye Gabas ta Tsakiya baki ɗaya yayin da ƙasarsa da Isra'ila suka fara kai mata hari
- Ya kuma ce Amurka ba ta cire yiwuwar tura sojojin musamman domin kwace sinadarin uranium da ya dade yana tsone masu ido
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
United States of America – Shugaban ƙasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa sabon jagoran da zai jagoranci Iran ba zai daɗe yana kan mulki ba.
Ya bayyana cewa matukar aka tabbatar da sabon shugaban ba tare da ya samu sahalewar Amurka ba, an yi aikin kawai.

Kara karanta wannan
Iran ta gargaɗi Amurka, ta faɗi abin da zai faru da jiragen da Trump zai tura Hormuz

Source: Facebook
Trump ya bayyana haka ne a wata hira da tashar talabijin ta ABC News, inda ya ce duk wanda zai zama sabon jagoran Iran dole ne ya samu amincewar Amurka
A ganinsa, wannan shi ne zai tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin Gabas ta Tsakiya.
Barazanar Trump ga sabon jagoran Iran
Al-Jazeera ta wallafa cewa Trump ya ce idan sabon jagoran Iran bai samu wannan amincewa ba, to akwai yiwuwar ba zai iya ci gaba da rike mulki na dogon lokaci ba.
Trump ya ce:
"Dole ne ya samu amincewarmu. Idan bai samu amincewarmu ba, ba zai daɗe a kan mulki ba.”
Trump ya kara da cewa burin Amurka shi ne tabbatar da cewa ba a sake komawa wani yanayi ba inda za a rika fuskantar irin wannan matsala duk bayan wasu shekaru.
Ya ce:
“Muna son mu tabbatar cewa ba za mu rika komawa bayan shekara 10 muna warware irin wannan matsala ba, musamman idan ba a samu shugaba irin ni ba da zai iya daukar irin wannan mataki ba."

Kara karanta wannan
Akwai matsala: Majalisar Dinkin Duniya ta hango abin da zai faru sakamakon yakin Amurka da Iran
Trump ya yi magana kan nukiliya a iran
Trump ya ce ba ya son a sake samun wani lokaci a nan gaba inda za a sake komawa ga irin wannan rikici, musamman idan har Iran ta samu makamin nukiliya.

Source: Twitter
Ya ce:
"Ba na son mutane su sake komawa bayan shekara biyar su sake yin irin wannan abu ko kuma mafi muni idan aka bari su samu makamin nukiliya.”
A cikin hirar, Trump ya kuma yi zargin cewa Iran na da wani shiri na mamaye yankin Gabas ta Tsakiya gaba ɗaya kafin Amurka ta dakatar da su.
Ya bayyana Iran a matsayin ƙasa mai nuna ƙarfi a fili amma a zahiri ba ta da irin wannan ƙarfin kamar yadda ake tunani.
Trump ya kuma bayyana cewa Amurka ba ta cire yiwuwar daukar karin matakan soja ba domin dakile barazanar da Iran ka iya kawowa.
A cewarsa, duk wata hanya na nan a bude, ciki har da yiwuwar tura sojojin musamman domin kwace sinadarin uranium mai ƙarfi da Iran ke da shi.

Kara karanta wannan
Shugaba Trump ya bayyana sharadi 1 tak da zai iya kawo karshen yakin Amurka da Iran
Switzerland ta yi tir da harin Amurka
A baya, kun ji Martin Pfister, Ministan tsaron Switzerland ya ce hare-haren Amurka da Isra’ila kan Iran sun karya dokokin ƙasa da ƙasa kamar yadda aka tanada.
Gwamnatin Switzerland ta bayyana cewa irin waɗannan hare-hare sun saɓa da dokar hana amfani da ƙarfi tsakanin ƙasashe kuma zai iya jawo babbar barazana.
Wasu manyan jami’an Turai da masana sun nuna shakku kan halaccin wannan yaƙi a dokokin duniya bayan Isra'ila da Amurka sun haɗa kai sun farmaki Iran.
Asali: Legit.ng