Amurka Ta Sha Mamaki, An Ruguza Mata Lissafi a Yaki da Jamhuriyar Musulunci Ta Iran

Amurka Ta Sha Mamaki, An Ruguza Mata Lissafi a Yaki da Jamhuriyar Musulunci Ta Iran

  • Iran ta bayyana cewa Amurka ta yi tunanin za ta kai mata farmaki kuma cikin kankanin lokaci za ta murkushe ta amma sai ta ga akasin haka
  • Babban sakataren Majalisar tsaro ta Iran, Ali Larijani ya lissafa abubuwa biyu da Amurka ta yi tsammani amma duka ba su samu ba
  • Larijani ya kuma soki shugaban Amurka, Donald Trump, kan maganarsa ta cewa Amurka za ta yi ruwa ta yi tsaki wajen zabar sabon jagoran Iran

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Iran - Kasar Iran ta yi ikirarin cewa Amurka ba ta yi tsammanin martani daga gare ta ba lokacin da ta kaddamar da harin farko a karshen watan Fabrairu, 2026.

Babban sakataren majalisar tsaron ƙasa ta Iran, Ali Larijani, ya bayyana cewa Amurka ta yi zaton cewa bugu daya za ta yi wa Iran ta samu nasara a kanta, amma sai ta ga akasin haka.

Kara karanta wannan

Iran ta gargaɗi Amurka, ta faɗi abin da zai faru da jiragen da Trump zai tura Hormuz

Trump da Khamenei
Shugaban Amurka, Donald Trump da marigayi Ayatollah Ali Khamenei Hoto: Hams Jaafar
Source: Getty Images

A rahoton da tashar Al-Jazeera ta dauko yau Asabar, Larijani ya bayyana abubuwa biyu da Amurka ta yi tsammanin za su ba ta nasara kan Iran idan ta fara kai hare-haren soji.

Abubuwan da Amurka ta yi tunani a Iran

Na farko, Ali Larijani, ya ce Amurka ta yi tunanin za ta iya zuwa cikin kankanin lokaci, ta farmaki Iran kuma ta samu nasara, amma wannan hasashe na ta ya zama kuskure.

Larijani ya bayyana cewa Amurka ta kuma yi zaton za ta iya haddasa rikici a cikin Iran ta hanyar kashe jagoran addini na kasar, Ayatollah Ali Khamenei, da wasu manyan shugabanni. Sai dai ya ce wannan tunani ma bai tabbata ba.

A cewarsa, duk da hare-haren hadin gwiwa da kasashen Isra'ila da Amurka suka kai, al’ummar Iran sun hada kai wajen kare kasarsu.

Gargadi ga kungiyoyin ‘yan aware

Larijani ya ce shugabannin Iran sun yi gargadi ga kungiyoyin ‘yan aware da kada su yi yunkurin tayar da rikici ko adawa da gwamnati a wannan lokaci na yaƙi.

Kara karanta wannan

Ba sauki: Iran ta kai hari mai zafi kan sansanin sojojin Amurka

Ya kara da cewa gwamnatin Iran na da tabbacin cewa al’ummar kasar sun hada kai wajen fuskantar hare-haren da kasashen biyu ke kai musu.

Iran ta kara sukar Shugaba Trump

Larijani ya kuma soki shugaban Amurka, Donald Trump, kan maganarsa ta cewa Amurka za ta yi ruwa ta yi tsaki wajen zabar sabon jagoran Iran.

Ya ce wannan ra’ayi 'wawanci ne', yana mai jaddada cewa Iran ba za ta amince da wani tsoma baki daga waje wajen zabar shugabanninta ba, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Har ila yau, Larijani ya sake jaddada matsayin Iran cewa ba za ta kai hari ga kasashen makwabta ba, matukar ba su bari a yi amfani da kasarsu wajen kai hari kan Iran ba.

Harin makami.
Yadda ake harba makami mai linzami a yakin Iran, Amurka da Isra'ila Hoto: Win Mac
Source: Getty Images

Iran za ta iya mika wuya ga Amurka?

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya maida martani ga Shugaban Amurka, Donald Trump, wanda ya nemi su mika wuya ba tare da sharadi ba.

Masoud Pezeshkian, ya bayyana cewa har abada Iraniyawa ba za su taba mika wuya ga Amurka ko Isra'ila ba, yana mai cewa ba za ta taba yuwuwa ba.

Wannan matsaya na zuwa ne sa'o'i 24 bayan shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya nemi Iran ta mika wuya ba tare da wani sharadi ba domin kawo karshen yakin da ya barke.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262