Saudiyya Ta Shiga Duniya Neman Kariya daga Hare Haren Iran

Saudiyya Ta Shiga Duniya Neman Kariya daga Hare Haren Iran

  • Ma'aikatar tsaron Saudiyya ta gana da shugaban sojojin Pakistan game da wata jarjejeniyar da kasashen suka kulla a shekarar 2025
  • Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da gwabza yakin Iran da Amurka/Isra'ila da ya shafi kasashe da dama a yankin Gabas ta Tsakiya
  • Ministan tsaron Saudiyya, Yarima Khalid bin Salman, ya yi magana game da fargabar yaduwar yakin zuwa kasashen da ba da su ake yi ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Pakistan - Ministan tsaron Saudiyya, Yarima Khalid bin Salman, ya bukaci Iran ta guji yin kuskure bayan harba makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuki zuwa cikin masarautar.

A cikin jerin sanarwa da ma’aikatar tsaron Saudiyya ta fitar ta ce ta dakile yunkurin harba makamai masu linzami sau da dama zuwa wani sansanin sojin sama da ke dauke da sojojin Amurka.

Kara karanta wannan

Yadda Rasha ke taimakon Iran wajen ragargazar dakarun Amurka a fagen yaki

Ministan tsaron Saudiyya da shugaban sojojin Pakistan
Ministan tsaron Saudiyya yayin ganawa da Shugaba sojojin Pakistan. Hoto: @kbsalsaud
Source: Twitter

Yarima Khalid bin Salman ya fitar da sanarwa a X game da tattunawa da ya yi da shugaban sojojin Pakistan a kan yakin da ya barke a Gabas ta Tsakiya.

Barazanar da kasar Saudiyya ke fuskanta

Iran na ci gaba da kai hare-hare a Gabas ta Tsakiya, mako guda bayan hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran wanda ya haifar da fadada rikicin zuwa yankin baki daya.

Saudiyya, wacce ita ce kasa mafi fitar da man fetur a duniya, ta ruwaito cewa a farkon makon nan an kai a kalla hare-haren jirage marasa matuka biyu da suka nufi matatar mai ta Ras Tanura da ke Gabashin kasar.

Iran: Saudiyya ta tafi kasar Pakistan

Yarima Khalid ya wallafa sako bayan ganawarsa da shugaban rundunar sojin Pakistan, inda ya ce sun tattauna kan hare-haren Iran kan Saudiyya da kuma matakan da ya kamata a dauka domin dakatar da su.

Kara karanta wannan

Makaman Iran sun dura kan tankar man Amurka a teku, ta kama da wuta

ND TV ta rahoto ya kara da cewa:

“Mun jaddada cewa irin wadannan matakai na kawo cikas ga tsaro da zaman lafiyar yankin, kuma muna fatan bangaren Iran zai yi amfani da hikima ya guji yin kuskure.”

Game da tsare Saudiyya daga hare-haren, Khalid bin Salman ya ce:

"Mun tattauna hare-haren Iran da matakan da ya kamata a dauka domin dakatar da su lura da yarjejeniyar da muka kulla."
Jami'an Saudiyya da Pakistan
Yadda aka gana tsakanin jami'an Saudiyya da Pakistan a 2025. Hoto: @kbsalsaud
Source: Twitter

Tun da farko ma’aikatar tsaron Saudiyya ta wallafa cewa:

“An tare wani makami mai linzami da aka harba zuwa Sansanin Sojin Sama na Yarima Sultan da ke kudu maso gabashin birnin Riyadh.”

Rasha na taimakon Iran kan Amurka

A wani rahoton, kun ji cewa wasu majiyoyi na zargin Rasha na taimakon Iran a yakin da ya shafe mako guda a yankin Gabas ta Tsakiya.

Majiyar ta ce Iran na samun taimakon bayanan sirri game da motsin sojoji, jiragen yaki da wasu kayayyaki da kadarorin Amurka.

A daya bangaren kuma, an bayyana cewa China na iya tallafawa Iran da kayan yaki, duk da cewa har yanzu ba a ce ta shiga yakin kai tsaye ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng