Ana Tsaka da Yaki, Trump Ya Yi Magana kan Kasancewar Iran a Gasar Cin Kofin Duniya

Ana Tsaka da Yaki, Trump Ya Yi Magana kan Kasancewar Iran a Gasar Cin Kofin Duniya

  • Kasar Iran ta cancanci shiga gasar cin kofin duniya ta shekarar 2026 wadda za a fafata a kasashen Amurka, Canada da Mexico
  • Yakin da ya barke tsakanin Amurka, Iran da Isra'ila, ya kawo kan yiwuwar kasancewar kasar a gasar wadda hukumar FIFA ke shiryawa
  • Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi magana kan yiwuwar kasancewar Iran a gasar buga kwallon kafan yayin da ake ci gaba da yaki

​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Kasar Amurka - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi magana kan yiwuwar kasancewar Iran a gasar cin kofin duniya na kwallon kafa ta shekarar 2026.

Trump ya bayyana cewa bai damu ba idan tawagar ƙwallon ƙafar ƙasar Iran za ta halarci gasar cin kofin duniya ta FIFA na 2026, a daidai lokacin da ake fuskantar rashin tabbas game da kasancewar kasar a gasar.

Kara karanta wannan

Khamenei: An ɗage taron jana'izar jagoran addini a Iran yayin da ake harin magajinsa

Donald Trump ya yi magana kan gasar cin kofin duniya
Shugaba Donald Trump da shugaban hukumar FiFA, Gianni Infantino Hoto: Patrick Smith
Source: Getty Images

Trump ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da tashar Politico a ranar Talata, 3 ga watan Maris 2026.

Kwallon kafa: Me Donald Trump ya ce kan Iran?

Shugaban kasar na Amurka ya bayyana cewa kasancewar Iran a gasar ba abu ba ne wanda ya dame shi.

"A gaskiya ban damu ba kan ko Iran za ta shiga gasar ko a'a. Ina ganin Iran ƙasa ce da aka yi nasara a kanta. Sun riga sun shiga cikin tarin matsaloli."

- Donald Trump

Tambayoyi sun taso game da kasancewar Iran a gasar sakamakon ƙaruwar takaddama a Gabas Ta Tsakiya da kuma fargabar ko za a amince wa jami’an Iran da magoya bayansu su shiga Amurka, wadda ita ce ɗaya daga cikin ƙasashen da za su karɓi baƙuncin gasar.

Ana gwabza yaki tsakanin Iran, Isra'ila da Amurka

A ranar Asabar ne Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar da hare-hare na haɗin gwiwa kan wasu wurare a Iran.

Kara karanta wannan

Asara ta fara bin Amurka, ta rasa biliyoyin Daloli kwanaki 5 da fara yakin Iran

Daga baya Iran ta mayar da martani da hare-haren makami mai linzami da na jirage marasa matuka kan sansanonin sojojin Amurka da na ƙawayenta a yankin tekun Fasha, wanda hakan ya tada fargabar ɓarkewar babban yaƙi a yankin.

Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya (FIFA) ta dade tana ƙoƙarin raba siyasa da wasan ƙwallon ƙafa na cin kofin duniya, wanda Amurka, Canada, da Mexico za su karɓi baƙunci a haɗe.

Iran ta cancanci zuwa gasar cin kofin duniya
Magoya bayan Iran a wajen wasan kwallon kafa Hoto: Ulrik Pedersen/DeFodi Images
Source: Getty Images

Iran ta cancanci zuwa gasar cin kofin duniya

A baya dai Iran ta riga ta isa zuwa gasar, inda aka tsara za ta fafata da tawagar ƙwallon ƙafar New Zealand, Belgium, da kuma Egypt a matakin rukuni.

Sai dai shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta Iran, Mehdi Taj, ya nuna cewa yanayin da ake ciki a halin yanzu zai iya shafar shirin ƙasar na shiga gasar.

Gasar cin kofin duniya ta 2026 ita ce gasa ta farko da ƙasashe uku za su karɓi baƙuncinta, kuma ana sa ran za ta jawo hankalin miliyoyin magoya baya daga ko’ina cikin duniya.

Amurka ta gargadi 'yan kasarta a Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa ofishin jakadancin Amurka a Najeriya, ya aika da sakon gargadi ga Amurkawa mazauna kasar.

Kara karanta wannan

Isra'ila ta fadi wani babba da ta ke shirin hallaka wa a kasar Iran

Ofishin ya sanar wa ‘yan kasarsa cewa akwai yiwuwar a gudanar da zanga-zanga a babban birnin tarayya Abuja saboda rikicin da ake ciki tsakanin Isra'ila, Amurka da Iran.

Hakazalika, ofishin ofishin ya kuma gargadi ‘yan kasar Amurka da su zauna a cikin gidajensu, su guji wuraren da ake tattaunawa ko za a yi gangami.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng