Asara Ta Fara Bin Amurka, Ta Rasa Biliyoyin Daloli Kwanaki 5 da Fara Yakin Iran
- An kiyasta cewa Amurka ta yi asarar kayan aikin soja da kudinsu ya kai kusan Dala biliyan 1.9 sakamakon hare-haren Iran
- Wani kayan aiki na 'Radar' mai darajar dala biliyan 1.1 a sansanin Al Udeid da ke Qatar na cikin manyan kayayyakin da aka lalata
- Iran ta kai hari kan sansanonin soja da ofisoshin jakadancin Amurka a kasashe da dama na Gabas ta Tsakiya bayan harin da aka kai mata
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
United States of America – Rahotanni sun nuna cewa Amurka ta yi asarar kusan Dala biliyan biyu na kayan aikin soja tun bayan da rikici ya barke tsakaninta da Iran.
Amurka da Isra'ila sun hada kai wurin kai wa kasar Iran hari a ranar 28 ga watan Fabrairu, 2026 inda aka kashe jagoran kasar, Ayatollah Ali Khamenei.

Source: Getty Images
TRT world ta wallafa cewa kididdigar da aka tattara sun nuna cewa hare-haren ramuwar gayya da Iran ta kaddamar sun janyo babbar asara ga kadarorin sojin Amurka a yankin.
Harin Iran ya jawo wa Amurka asara
Anadolu Ajasi ta ruwaito cewa babban abin da ya fi jawo asarar shi ne na'urar gargadi wato radar na farko mai suna AN/FPS-132 da ke sansanin Al Udeid Air Base a Qatar, wanda kudinsa ya kai dala biliyan 1.1.
An harba makami mai linzami da ya bugi na’urar a ranar Asabar. Mahukuntan Qatar sun tabbatar da cewa an samu lahani mai tsanani a kan na'urar.

Source: Facebook
A ranar Lahadi 1 ga watan Maris, 2026 kuma, jiragen yaki uku kirar F-15E Strike Eagle sun lalace sakamakon kuskuren harbo shi da aka yi a samaniyar Kuwait.
Duk da cewa duka matukan jiragen shida sun tsira da rayukansu, jiragen sun lalace gaba daya, kuma ana kiyasta kudin maye gurbinsu ya kai Dala miliyan 282.

Kara karanta wannan
Yadda kisan Khamenei zai shafi 'yan Shi'a a Najeriya, rashinsa ya 'hada' kan Musulmi
An kai hare-hare sansanonin Amurka
A harin farko na ramuwar gayya, Iran ta kai farmaki hedikwatar rundunar Fifth Fleet ta sojojin ruwan Amurka da ke Manama, Bahrain.
A yayin harin an lalata na’urorin sadarwar tauraron dan adam guda biyu da wasu manyan gine-gine.
Rahotannin bincike sun nuna cewa na’urorin AN/GSC-52B ne, kuma kudinsu ya kai kusan Dala miliyan 20.
Iran ta kuma ce ta lalata wani bangare na na'uarar 'radar AN/TPY-2' na tsarin kariyar makamai masu linzami na THAAD da aka girke a Al-Ruwais a Hadaddiyar Daular Larabawa.
Hotunan tauraron dan adam sun nuna alamun an lalata wurin, kuma ana kiyasta darajar bangaren da aka lalata ya kai Dala miliyan 500.
Isra'ila na fakon babba a Iran
A baya, mun wallafa cewa Ministan tsaron Isra’ila, Israel Katz ya yi barazana ga sabon Ayatollah, wato jagoran addini da Iran ke shirin nada wa bayan hallaka Ali Khamenei.
Ministan tsaron ya bayyana cewasun yi shiri na musamman domin a kawar da duk sabon shugaban da jamhuriyyar Musulunci ta Iran za ta nada da hadin gwiwar Amurka.
Ya jaddada cewa Isra’ila za ta hada kai da Amurka domin lalata karfin Iran yayin da ake ci gaba da samun musayar wuta a tsakanin kasashen bayan hallaka Khameini.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
