Rana Ta 5: Iran Ta Zafafa Hare Hare kan Amurka, Ta Harba Makamai Masu Linzami 40
- Iran ta harba makamai masu linzami guda 40 kan sansanonin Amurka da Isra'ila a matsayin rukuni na 17 na daukar fansa
- Rundunar CENTCOM dai ta bayyana cewa ta ruguza hedkwatar dakarun IRGC domin gurgunta karfin sojin Iran a wannan yaki
- A hannu daya, Ministan tsaron Isra'ila ya yi barazanar cewa za su kashe duk wani wanda aka zaba domin ya maye gurbin Khamenei
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Iran - Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC) sun da cewa sun harba akalla makamai masu linzami guda 40 wadanda suka nufi sansanonin Amurka da Isra'ila.
Wannan shi ne rukuni na 17 na farmakin da suka kira "Honest Promise 4," wanda martani ne ga kisan gillar da aka yi wa tsohon jagoran addinin kasar, Ayatollah Ali Khamenei, a ranar Asabar.

Source: Getty Images
Iran ta farmaki sansanonin Amurka/Isra'ila
Sanarwar, wadda aka karanta a gidan talabijin na kasar, ta jaddada cewa "guguwar daukar fansa" ba za ta taba kyale wadanda suka kashe 'Jagoran Al'umma' ba, in ji rahoton Aljazeera.
A daidai lokacin da farashin makamashi ke tashi a fadin duniya sakamakon fadadar yakin, dakarun IRGC sun yi ikirarin cewa suna da "cikakken iko" akan mashigar ruwa ta Hormuz.
Wannan mashiga ita ce jigon tattalin arzikin duniya, kuma barazanar rufe ta na jefa kasuwannin duniya cikin rudani.
Amurka ta ruguza hedikwatar IRGC
Saboda tsananin ruwan wutar, kasashen duniya ciki har da Biritaniya da Faransa sun fara tura jiragen haya na musamman domin kwashe 'yan kasarsu dake makale a Gabas ta Tsakiya.
A gefe guda kuma, rundunar sojin Amurka ta CENTCOM ta tabbatar da cewa ta ruguza babban ofishin dakarun IRGC a wani gagarumin hari da ta kai, in ji rahoton France 24.
CENTCOM ta bayyana wannan mataki a matsayin "yanke kan maciji," inda ta zargi dakarun da hannu wajen kashe Amurkawa sama da 1,000 a cikin shekaru 47 da suka gabata.
Ya zuwa yanzu, sojin Amurka sun ce sun daki wurare kusan 2,000 a kasar Iran tun bayan fara fafatawa a ranar Asabar.

Source: Twitter
Barazanar kisa ga sabon jagoran Iran
Hakazalika, Ministan Tsaron Isra'ila, Israel Katz, ya fitar da sanarwa mai zafi a shafinsa na X, inda ya yi barazanar cewa duk wani jagora da Iran za ta zaba domin maye gurbin Khamenei zai fuskanci kisa.
Katz ya jaddada cewa duk wanda aka nada domin cigaba da shirin ruguza Isra'ila ko yi wa Amurka barazana, za su kaddamar da harin kisa a kansa ko ina ya boye.
Amurka ta sake yin kira ga dukkan 'yan kasarta dake yankin da su fice cikin gaggawa ta hanyar jiragen 'yan kasuwa, kodayake zirga-zirgar jiragen sama ta durkushe sakamakon hare-haren da bangarorin biyu ke kaiwa juna.
Iran ta farmaki ofishin jakadancin Amurka
A wani labari, mun ruwaito cewa, wani jirgin marar matuki ya daki ofishin jakadancin Amurka a Dubai inda aka samu tashin gobara a ranar Talata.

Kara karanta wannan
Yadda kisan Khamenei zai shafi 'yan Shi'a a Najeriya, rashinsa ya 'hada' kan Musulmi
Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya tabbatar da cewa an kwashe kusan Amurkawa 9,000 daga Gabas ta Tsakiya.
A harin da Iran ta kai ofishin jakadancin Amurka, an ga bidiyon yadda wuta ke ci gadan gadan yayin da yakin ya shiga rana ta hudu.
Asali: Legit.ng

