Bidiyon yadda Wuta Ke Ci Gadan Gadan a Ofishin Amurka bayan Iran Ta Kai Hari
- Wani jirgin marar matuki ya daki ofishin jakadancin Amurka a Dubai inda aka samu tashin gobara kodayake babu asarar rayuka
- Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya tabbatar da cewa an kwashe kusan Amurkawa 9,000 daga Gabas ta Tsakiya
- A harin da Iran ta kai ofishin jakadancin Amurka, an ga bidiyon yadda wuta ke ci gadan gadan yayin da yakin ya shiga rana ta hudu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Dubai - An shiga firgici a birnin Dubai dake ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), inda aka ruwaito cewa wani jirgin marar matuƙi ya daki ofishin jakadancin Amurka.
Hukumomin Dubai sun tabbatar da cewa wuta ta tashi sakamakon wannan hari da ya afku a filin ajiye motoci kusa da babban ginin ofishin, amma tuni jami'an kashe gobara suka shawo kan lamarin.

Kara karanta wannan
Ronaldo ya lallaɓa ya bar Saudiyya saboda rikicin Isra'ila, Iran? an ji gaskiyar zance

Source: Getty Images
Iran ta farmaki jakadancin Amurka a Dubai
Wannan harin ya ƙara ruruta wutar fargabar ɓallewar yaƙin duniya na uku (WWIII) yayin da rikicin Gabas ta Tsakiya ke ci gaba da ta'azzara, in ji rahoton Aljazeera.
Ofishin yaɗa labaran Dubai ya sanar da cewa "babu wani rauni ko asarar rai da aka samu" a wannan hari da aka yi amfani da jirgi marar matuki.
Bidiyon da suka karade soshiyal midiya da aka tantane sun nuna hayaki na tashi daga yankin ofishin jakadancin.
Wannan harin na zuwa ne jim kaɗan bayan an kai makamancinsa a ofishin jakadancin Amurka dake birnin Riyadh na ƙasar Saudi Arabia, inda aka samu ɓarna amma babu asarar rai.
Iran na ci gaba da kai wa Amurka hare-hare a matsayin fansar harin ranar Asabar, wanda ya yi ajalin jagoran addininta, Ayotallah Ali Khamenei.
Kwashe matafiya daga kasar UAE
Sakamakon wannan barazana, Ministan Tattalin Arziki da Yawon Buɗe Ido na UAE, Abdulla Bin Touq Al Marri, ya sanar da cewa za a fara kwashe matafiya sama da 44,000 daga ƙasar zuwa ƙasashensu.

Kara karanta wannan
Hadimin Tinubu ya tsoma baki a yakin Iran da Amurka, ya tura sako Majalisar dinkin duniya
Matakin farko ya haɗa da kwashe fasinjoji kusan 17,500 a cikin jirage 60, yayin da mataki na biyu zai kwashe wasu mutane 27,000.
Wannan na nuna yadda harkar sufurin jiragen sama ta durƙushe sakamakon ruwan wutar da ake yi a yankin Gabas ta Tsakiya, in ji rahoton Peninsula Qatar.

Source: Getty Images
Amurka ta kwashe mutanenta daga Gabas ta Tsakiya
A ɓangaren Amurka kuma, Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya bayyana cewa kusan Amurkawa 9,000 aka kwashe daga Gabas ta Tsakiya tun farkon fara yaƙin yau.
Rubio ya tabbatar da cewa dukkan ma'aikatan ofishin jakadancin Amurka dake Dubai suna nan cikin ƙoshin lafiya bayan harin yanzu.
Ya ƙara da cewa akalla Amurkawa 1,600 ne ke ci gaba da neman taimakon gaggawa domin ficewa daga yankin da ake rikicin.
Kalli bidiyon gobarar da ta tashi a ofishin jakadancin Amurka a Dubai, da wasu ma'abota shafukan X suka wallafa a kasa:
Iran ta farmaki Amurkawa a Saudiyya
A wani labari, mun ruwaito cewa, an shiga rana ta hudu a yaki tsakanin Amurka/Isra'ila da Iran, inda aka kai hari ofishin Jakadancin Amurka a Saudiyya.
Rahotanni sun nuna cewa Amurka ta fitar da sanarwa game da 'yan kasarta da ke zaune a kasar Saudiyya bayan harin da Iran ta kai ofishinta.
Shugaba Donald Trump ya nuna damuwa game da harin, inda ya bayyana cewa nan gaba kadan duniya za ta ga martanin da Amurka za ta yi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
