Ana tsaka da Musayar Wuta, Iran Ta Samu Gagarumin Goyon Baya a Yaki da Amurka da Isra'ila
- Kasar China ta fito fili ta bayyana goyon bayanta a yakin da ya barke tsakanin Iran da kasashen Amurka da Isra'ila
- Ministan harkokin wajen China, Wangi Yi ya shaida wa takwaransa na Iran cewa suna goyon bayan kokarin Iran na kare kanta daga Amurka
- Ya kuma zargi Amurka da Isra'ila da karya ka'idoji da dokar Majalisar Dinkin Duniya, tana mai cewa kamata ya yi a koma teburin sulhu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
China - Ministan harkokin wajen China, Wangi Yi, ya tattauna ta wayar salula da takwaransa na kasar Iran, Abbas Araghchi, yau Litinin, 2 ga watan Maris, 2026.
Wangi Yi ya shaida wa takwaransa na Iran cewa China na goyon bayan Jamhuriyar Musulunci wajen kare kanta daga hare-haren Amurka da Isra'ila, yayin da yakin ke kara yaduwa a Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan
Bayan kashe 'dan kasarta, China ta maida martani kan yakin Iran da Amurka, Isra'ila

Source: Getty Images
Tashar Al-Jazeera ta tattaro cewa daruruwan mutane sun mutu a Iran tun daga ranar Asabar lokacin da Amurka da Isra’ila suka fara kai hare-hare kan wurare da dama a kasar.
Tehran ta mayar da martani ta hanyar harba makamai masu linzami da jiragen yaki marasa matuki zuwa Isra’ila, kasashen Gulf da kuma wani sansanin Birtaniya a Cyprus.
China ta bayyana goyon baya ga Iran
Wangi ya ya gaya wa ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, cewa:
“Kasar China na daraja tsohuwar abotar da ke tsakaninta da Iran, don haka tana goyon bayan Iran wajen kare ’yancinta, tsaronta, cikakken ikon yankinta da martabarta ta kasa.
"China na goyon bayan Iran wajen kare hakkokinta da muradunta na halal."
Wangi ya kara da cewa China “ta bukaci Amurka da Isra’ila da su dakatar da kai hare-hare, su guji kara tayar da hankali, kuma su hana rikicin yaduwa zuwa daukacin yankin Gabas ta Tsakiya."
China ta soki matakin Amurka da Isra'ila
A wata tattaunawar daban da ministan harkokin wajen Oman a ranar Litinin, Wangi ya zargi Amurka da Isra’ila da “karya manufofi da ka’idojin kundin tsarin Majalisar Dinkin Duniya” ta hanyar “kaddamar da yaki da gangan kan Iran.”
“Ba zai yiwu a bari manyan kasashe su rika kai hare-hare suna zaluntar kananun kasashe bisa karfin sojinsu kawai ba,” in ji ministan.

Source: Getty Images
Ya kuma jaddada cewa ya zama dole a rungumi tattaunawa ta diflomasiyya domin warware batun shirin nukiliyar Iran wanda ake ta ce-ce-ku-ce.
Ya zuwa yanzu, sojojin Amurka hudu sun mutu a fadan, yayin da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya gargadi cewa yakin da Iran na iya daukar makonni da dama, cewar Vanguard.
Iran ta aika wasika Majalisar Dinkin Duniya
A wani rahoton, kun ji cewa ministan harkokin wajen ƙasar Iran, Abbas Araghchi, ya yi Allah-wadai da farmakin soji da Amurka da Isra’ila suka kai wa ƙasarsa.
A cikin wasiƙar da ya aike wa Majalisar Ɗinkin Duniya, Araghchi ya bayyana harin a matsayin abin da ya sabawa ƙa’idojin da ke jagorantar hulɗar ƙasashe.
Iran ta bayyana cewa tana da ikon kare kanta kuma za ta yi hakan ba tare da shiga wata tattauna wa ko yarjejeniya da Amurka ba.
Asali: Legit.ng

