Macron Ya Fadi Shirin da Faransa ke Yi bayan Amurka da Isra'ila Sun Kai wa Iran Hari

Macron Ya Fadi Shirin da Faransa ke Yi bayan Amurka da Isra'ila Sun Kai wa Iran Hari

  • Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce rikici tsakanin Amurka da Isra’ila da Iran na barazana ga zaman lafiya a duniya
  • Shugaban ya yi kira da a kauce wa yaƙi, a koma kan teburin tattaunawa domin a kai ga matakin sulhu don kauce wa asarar rayuka
  • Ya bayyana cewa kasarsa ta shirya daukar matakin da ta ke ganin ya dace, yayin da aka fara tuntubar masu ruwa da tsaka a lamarin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. France – Shugaban ƙasar Faransa, Emmanuel Macron, ya bayyana cewa yiwuwar ɓarkewar yaƙi tsakanin Amurka, Isra'ila da Iran na da matuƙar haɗari ga zaman lafiya da tsaron duniya baki ɗaya.

Macron ya ce duk wata arangama kai-tsaye tsakanin waɗannan ƙasashe uku za ta iya haddasa rikici mai faɗi wanda zai shafi yankin Gabas ta Tsakiya da ma sauran sassan duniya.

Kara karanta wannan

Dalilai 3 da suka jawo Tinubu ya umarci Sufeton yan sanda ya yi murabus

Macron na son Iran da Isra'ila da Amurka su koma teburin sulhu
Shugaban Iran Masoud Pezeshkian Emmanuel Macron na kasar Faransa Hoto: Getty
Source: Getty Images

A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Emmanuel Macron ya ce halin da ake ciki yanzu na buƙatar a bi a hankali da kauce wa duk wani mataki da zai iya rura wutar rikici.

Gargadin Macron kan yakin Isra'ila da Iran

Macron ya bayyana cewa ƙara tsananta rikici zai iya jefa fararen hula cikin mawuyacin hali, tare da lalata tattalin arziki da samar da sabon yanayi na rashin tabbas a duniya.

Shugaban na Faransa ya jaddada muhimmancin tattaunawa a matsayin hanya mafi dacewa ta warware sabani.

Netanyahu da Trump sun hada baki, sun kai wa Iran hari
Firayim Ministan Isra'ila Benjamin Netanyau tare da Donald Trump Hoto: Getty
Source: Getty Images

Macron ya kuma nuna cewa kasashen duniya na da alhakin kare zaman lafiya, musamman a lokacin da ake fuskantar barazanar da ka iya haddasa rikicin yaƙi mai girma.

Ya ce lokaci ne na daukar matakai a cikin hankali domin kauce wa zubar da jini da tashin hankali.

Matakan da Faransa ke dauka - Macron

A jawabin nasa, Macron ya yi kira ga shugabannin ƙasashen da abin ya shafa da su fifita diflomasiyya maimakon farmaki.

Kara karanta wannan

Zargin kashe Kiristoci: Matakai 6 da ake son Trump ya ɗauka a kan Najeriya

Ya ce dole ne a ba tattaunawa da sulhu dama domin dakile yiwuwar ɓarkewar yaƙin da zai kazanta da kara asarar rayuka.

Macron ya nuna cewa Faransa za ta ci gaba da aiki tare da ƙawayenta domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Ya bukaci a rage zafafan kalamai da matakan soja, tare da ba da dama ga hanyoyin sasanci inda ya ce kasarsa ta fara magana da kawayenta a Turai da Gabas ta Tsakiya. Shugaban ya jaddada cewa duniya na cikin wani yanayi mai sarkakiya, don haka ya kamata shugabanni su guji duk wani abu da zai kara rura wutar rikici.

Rikicin Iran da Isra'ila ya shafi Saudiyya

A baya mun wallafa cewa rahotanni sun ce an ji karar fashe-fashen abubuwa a Riyadh, Dubai da Abu Dhabi bayan Iran ta harba makamai masu linzami a matsayin martani ga Isara'ila.

Mahukuntan Hadaddiyar Daular Larabawa sun tabbatar da hana wasu makamai masu linzami sauka, inda rahotanni suka ce mutum guda ya mutu a Abu Dhabi da ke kasar

Hare-haren sun zo a matsayin ramuwar gayya bayan hare-haren hadin gwiwa da Isra'la da Amurka suka kai kan Iran, lamarin da ya kara dagula tsaro a yankin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng