Kasashen Musulmi 2 Sun Kaure da Yaki, an Yi Ruwan Bama Bamai
- Kasar Pakistan ta bayyana cewa ta kaddamar da hare-hare zuwa Afghanistan, inda ta kara da cewa yaki ya barke a tsakaninsu
- Tsohon shugaban Afghanistan, Hamid Karzai ya tabbatar da aukuwar hare-haren, inda ya ce ba za su zuba ido ba, za su yi martani
- Rahotanni sun nuna cewa kasashen biyu sun dade suna zaman doya da manja da ya kai ga kai hare-hare da suka jawo rasa rayuka
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Pakistan - Ministan tsaron Pakistan, Khawaja Asif ya bayyana cewa an shiga yaki kai tsaye tsakanin Pakistan da gwamnatin Taliban ta Afghanistan, yayin da aka ruwaito fashe-fashe a Kabul kuma fada ke cigaba a kan iyaka.
Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif ya ce sun dade suna neman zaman lafiya, amma yanzu sojojin kasar za su fuskanci duk wani hari da kakkausan martani.

Source: Getty Images
Rahoton tashar Al-Jazeera ya nuana cewa tsohon shugaban Afghanistan ya tabbatar da cewa an kai hare-haren bama-bamai wasu yankunan kasarsa.
Pakistan ta kai hari Afghanistan
Tsohon shugaban Afghanistan, Hamid Karzai ya ce jiragen saman Pakistan sun kai hare-haren bama-bamai a Kabul, Kandahar da Paktia a Afghanistan.
“‘Yan Afghanistan za su kare kasarsu da cikin hadin kai a kowane hali, kuma za su mayar da martani ga duk wani hari,”
Inji tsohon shugaban.
Ya kara da cewa:
“Pakistan ba za ta kubuta daga tashin hankali da hare-haren bama-bamai ba — matsalolin da ita da kanta ta haddasa — sai ta sauya manufofinta tare da zabar hanyar kyakkyawar makwabtaka, mutunta juna da dangantaka mai kyau da Afghanistan.”
Maganar minista tsaron Pakistan
Biyo bayan hare-haren, Ministan tsaron kasar Pakistan, Khawaja Asif ya ce yaki kai tsaye ya barke tsakanin Pakistan da Afghanistan.
A wani sako da ya fitar, ministan ya zargi hukumomin Taliban na Afghanistan da tara ’yan ta’adda da kuma ta’addanci, tare da hana ‘yan Afghanistan — musamman mata — hakkokinsu da kuma zama wakilin kasar Indiya.
“Yanzu yaki ne kai tsaye tsakaninmu da ku… Sojojin Pakistan ba su nesa da ku. Mu makwabtanku ne; mun san dukkan sirrinku,”
Inji shi

Source: AFP
Sa’o’i kafin Pakistan ta kai harin sama a Kabul, ma’aikatar watsa labaran Islamabad ta zargi hukumomin Taliban na Afghanistan da bude wuta a wurare da dama da ke kan iyakar Arewa maso Yammacin kasashen biyu.
Mai magana da yawun gwamnatin Taliban, Zabihullah Mujahid ya tabbatar da harin da Pakistan ta kai a wani sako da ya wallafa a X, ya ce ya shafi wurare uku.
An so kai hari masallaci a Birtaniya
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Birtaniya ta tabbatar da kama wani bature da makami ya yi yukurin shiga masallacin Manchester.
'Yan sanda sun tabbatar da kama shi tare da cewa an tsaurara tsaro a masallatai kuma ana cigaba da yi wa wanda aka cafke tambayoyi.
Firaministan Birtaniya ya ce abin takaici ne yunkurin kai hari a Ramadan kuma ya ware makudan kudi domin kara tsaro a wuraren ibadar Musulmi.
Asali: Legit.ng

