An ‘Gano’ Musabbabin Hari kan Musulmi bayan Farmaki ana Sallar Asham a Ramadan
- An kai hari domin kona ginin cibiyar al’ummar Musulmi da gangan kusa da sabon masallaci a Worcester, Birtaniya
- Ƙungiyar 'Worcester Muslim Welfare Association' ta ce harin ya jefa al’umma cikin matsanancin damuwa a watan Ramadan
- Lamarin ya biyo bayan wani hari a masallacin Manchester, inda aka kama mutum ɗaya yayin da ake farautar wani da ake zargi
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Worchester, England - Wata cibiyar al’ummar Musulmi da ke kusa da sabon masallaci a garin Worcester ta magantu kan harin da aka kai.
An kai harin ne a yankin Yammacin Midlands na ƙasar England wanda ya fuskanci abin da aka bayyana a matsayin “tayar da gobara da gangan.”

Source: Getty Images
Musulmai sun magantu kan hari a cibiyarsu
Ƙungiyar Worcester Muslim Welfare Association (WMWA) ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis 26 ga watan Fabrairun 2026 wanda shafin @5Pillarsuk ya wallafa a X.
A cikin sanarwar, kungiyar ta ce wani namiji ne ya kai harin da safe, inda ya nufi ginin al’umma da ke kusa da masallacin.
A cewar ƙungiyar, ginin da aka kai wa harin shi ne 'Unity House Community Hub' da ke kan titin Stanley a Worcester, wanda aka ƙona da gangan.
Bidiyoyi da ke yawo a kafafen sada zumunta sun nuna wani mutum yana kunna wuta kusa da ginin kafin ya tsere daga wurin.

Source: Facebook
Matakin farko da Musulmi suka dauka
Ƙungiyar ta ce ta kai rahoton lamarin ga rundunar 'yan sanda na Yammacin Mercia, tana mai cewa harin ya haddasa “mummunar damuwa a tsakanin al’ummarmu.”
Sanarwar ta ƙara da cewa:
“Ba za mu iya kallon wannan lamari a matsayin abu daban ba."
“Mun yi imanin cewa wannan hari ne na ƙiyayya mai tushe a kan wariyar launin fata da addini da ake yawan kai wa Musulmi.”
Kungiyar ta ce tana mai tunatar da cewa lamarin ya faru ne a cikin watan Ramadan mai alfarma bayan wani mummunan hari da aka kai a wani hari a masallaci a Manchester.
Ƙungiyar ta ce tana da yakinin cewa harin na ɗauke da ƙiyayya ta ɓangaren launin fata da addini, watau 'Islamophobia'.
A Manchester kuwa, ‘yan sanda sun kama mutum ɗaya tare da fara farautar wani a ranar Laraba 26 ga watan Fabrairun shekarar 2026 bayan kai harin.
Hakan ya biyo bayan zarginsa da shigar da makamai ciki har da gatari da wuka a cikin babban masallacin Manchester yayin sallar Tarawihi.
Firayim minista ya magantu kan hari a masallaci
A wani labarin, Firayim ministan Birtaniya, Keir Starmer ya yi magana game da wani mutum da aka kama da makami yana shirin shiga masallaci a birnin Manchester.
Keir Starmer ya bayyana matakan tsaro da za a cigaba da dauka a masallatai domin kare Musulmai masu ibada, musamman a watan azumin Ramadan.
Jami'an tsaron Birtaniya sun bayyana cewa ana yi wa wanda aka kama tambayoyi domin sanin dalilin yunkurin shiga masallaci da makamai a Birtaniya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

