Dan Bindiga Ya Harbe Amurkawa har Lahira bayan Trump Ya Turo Sojoji Najeriya
- Rahotanni sun nuna cewa wani dan bindiga dauke da makami ya yi harbin kan me uwa da wabi a wani filin wasa bayan jama'a da dama sun taru
- Harbin da ya yi ya jawo asarar rayuka nan take yayin da wasu suka rasu a asibiti yayin da likitocin da ke aiki suka yi kokarin ceto rayuwarsu
- Hakan ya zo ne bayan gwamnatin shugaba Donald Trump ta aika da sojoji kimamin 100 Najeriya a cewa za su horas da sojojin kasar wasu abubuwa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Amurka - Mutum uku sun mutu sakamakon harin dan bindiga a wani filin wasa a kasar Amurka, kamar yadda hukumomi suka bayyana.
Harbin ya auku ne a Dennis M. Lynch Arena da ke Pawtucket, kusa da Providence a jihar Rhode Island, da misalin ƙarfe 2:30 na rana a ranar Litinin, 16 ga Fabrairun 2026.

Source: Getty Images
Rahoton da Sky News ta wallafa ya bayyana cewa dan bindigar ya bude wuta ne ana shirin fara wasan hockey na matasa a filin.
Wanda ya kai harin ya mutu
Wanda ake zargi da ’yan sanda suka bayyana sunansa a matsayin Robert Dorgan na cikin mutanen uku da suka mutu a harin.
'Yan sanda sun ce Dorgan da aka fi sani da Roberta Esposito, ya mutu ne sakamakon raunukan harbin bindiga da ya same shi yayin da ya ke harbe mutane.
Rahotanni sun nuna cewa shugabar ’yan sandan Pawtucket, Tina Goncalves ta ce an haifi Dorgan a shekarar 1969, amma ba ta bayar da ƙarin bayani ba.
Mutanen da aka harbe a Amurka
Tina Goncalves ta ƙara da cewa mutanen biyu da aka harbe suka mutu manya ne. An samu gawar ɗaya a cikin filin wasan, yayin da ɗayan ya mutu a asibiti.
Rahoton Al-Jazeera ya bayyana cewa wasu mutum uku kuma sun samu raunukan harbin bindiga, kuma a halin yanzu suna cikin mawuyacin hali a asibiti.
’Yan wasa da magoya baya sun ruga neman mafaka bayan jin ƙarar harbe-harbe a wurin, kamar yadda wani bidiyo ya nuna.
Kalli bidiyon kai harin a kasa:
Mutane sun rusa kuka a Amurka
An ga mutane na zubar da hawaye da ’yan wasan makarantar sakandare suna rungumar juna a wajen filin bayan harin, yayin da ’yan sanda suka kewaye wajen.
Goncalves ta tabbatar da cewa akwai mutane da dama na cikin filin wasan lokacin da harin ya faru, sai dai da dama ba su samu rauni ba.

Source: Getty Images
Harin na zuwa ne kusan wata biyu bayan wani ɗan bindiga ya kashe mutum uku da ya buɗe wuta a Jami’ar Brown da ke Providence.
Tambayoyi kan tura sojin Amurka Najeriya
A wani labarin, mun kawo muku cewa gwamnatin Najeriya ta fara shan tambayoyi game da sauke sojojin Amurka a jihar Bauchi.
Audu Bulama Bukarti ya bukaci gwamnatin kasar ta fito da bayanai game da tsawon lokacin da sojojin za su zauna a Najeriya.
Ya bukaci karin bayani kan dalilin sauke sojojin a Bauchi maimakon Zamfara, Neja ko Borno da ke fama da ta'addanci kai tsaye.
Asali: Legit.ng

